Connect with us

Labaran Najeriya

An sace kakakin jagoran hidimar siyasar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Muna ‘yan lokatai kadan da fara jefa kuri’a ga zaben shugaban kasa da gidan majalisai ta shekarar 2019, don zaban sabbin shugabannana da za su jagoranci kasar Najeriya a tsawon shekaru hudu da nan, sai gashi an sace Mista Austin Okai, kakakin hidimar zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ta jihar Kogi.

Jam’iyyar PDP a jihar na zargin cewa ‘yan adawan su, jam’iyyar APC ne suka aiko da ‘yan ta’adda a daren ranar jumma’a da ta gabata don sace Mista Austin kamin gari ya waye.

Mista Kola Ologbondiyan, kakakin jam’iyyar PDP na tarayya, ya bukaci IGP Adamu Mohammed, shugaban jami’an tsaron ‘yan sandan kasar Najeriya da cewa ya watsar da jami’an tsaro a hanyar da ta bi Banda, Lokoja har zuwa Abuja don bincike da ganin cewa an ribato Mista Austin daga wannan harin.

“Idan ba a ribato ko kubuto da Mista Austin Okai daga hannun wadanan ‘yan ta’addan ba, abin zai tada farmaki kwarai da gaske, musanman ga matasa da daman suna jiran ta baci ne su dauki mataki da kansu” inji Kola.

Mun iya ganewa a Naija News Hausa da  cewa cikin makonnai biyu zuwa ukku da suka gabata, mun ruwaito da rahoton sace-sacen ciyamomin jam’iyya da dama a kasar, har ma akwai wadanda aka kashe daga cikin su.

Wannan abi takaici ne ganin ga zaben kasar ta gabato cikin ‘yan kalilan awowi.

Jam’iyyar PDP sun kara bayyana da cewa an sace ciyamomin kananan yankuna a Jihar Rivers, da zargin cewa sojoji ne suka aiwatar da hakan a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

“Haka kuma aka kame mana shugabannan jam’iyyar a Jihar Kano, kamar dan takaran Sanata, Ahmed Haruna Bichi dan takaran Gidan Majalisar Jiha, Hon. Ahmed Garba Bichi” inji PDP.

“Mun kira ga al’ummar Najeriya da su kula da yadda shugabancin Muhammadu Buhari ke tsananta wa ‘yan kasa, musanman mambobin jam’iyyar adawa” inji su.

Karanta wannan kuma: Yan Sandan sun kame Sanata Rafiu Ibrahim a Jihar Kwara