Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli bayani mutane game da yadda Buhari ya leki zaben matarsa Aisha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Najeirya sun mayar da martani game da yadda shugaba Muhammadu Buhari ya kalli matarsa Aisha a lokacin da take jefa kuri’ar ta.

Mun ruwaito da safen da cewa shugaban hade da matarsa sun jefa kuri’a su a filin zabe.

Nigerians React To Buhari Spying Aisha’s Ballot Paper

Ko da shike ba a gane dalilin da yasa shugaban ke lekan takardan zaben matarsa ba, amma mun iya gane wa a Naija News Hausa da cewa watakila shugaban na kokari ya leka ne don gane ko waye matarsa ta jefa wa kuri’ar ta.

Muna da tabbaci ne da cewa shugaban da matarsa sun jefa kuri’ar su ne da safen nan misalin karfe 8:03 a kauyan Daura ta Jihar Katsina.

Shugaban kuma ya jefa na sa kuri’ar misalin karfe 8:07 na safiya.

Bayan sun bar wajen ne aka wallafo bidiyon yadda shugaban ya ke lekar matansa a yayin da take dangwala yatsar ta ga takardan zaben ta.

A halin yanzun bidiyon yadda shugaban ya leki takardan matansa ya mamaye ko ta ina a yanar gizo.

Kalli bidiyon a kasa;

https://twitter.com/chosensomto/status/1099214267755253760