Connect with us

Uncategorized

PDP: Kalli lokacin da Atiku Abubakar da matarsa Titi suka jefa kuri’ar su

 

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar tare da matarsa a yau sun fita don jefa na su kuri’ar ga zaben shugaban kasa da ta gidan majalisai.

Mun ruwaito a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Muhammadu Buhari sun jefa na su kuri’ar misalin karfe 8:07 na safiyar nan. Inda aka bayyana a wata bidiyo da cewa shugaban ya leki takardan matansa don gane ko wani jam’iyyar ta zaba.

Atiku da Titilato su ma sun fita don su jefa ta su kuri’a a matsayin ‘yan kasa da kuma dan takara.

Mun samu rahoto ne a Naija News da cewa dan takaran da matarsa sun sami isa runfar zaben ne da ke a birnin Yola misalin karfe 9:58 na safiya.

Bayan isarsu kuma sun shiga kan layi don daukar nasu takarda don dangwala yatsa da kuma saka kuri’ar a cikin akwatin zabe kamar yadda kowa ke yi.

A daidai karfe 10:04 na safiyar Atiku da Titi suka gama hidimar zaben su kamin suka bar runfar zabe don kama hanyar su.

Karanta wannan kuma: An gano wata motar daukan kudi na shiga kofar gidan shugaban Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a jihar Legas.

Advertisement
close button