Gona mai kimanin ajiyar hatsi fiye da naira Miliyan daya (N1m) ya kame da wuta | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

Gona mai kimanin ajiyar hatsi fiye da naira Miliyan daya (N1m) ya kame da wuta

Published

Hatsi na kimanin kudi Miliyan daya (N1m) ta kame da wuta a Jihar Jigawa

Wata babban gonar ajiyar hatsi da ke a kauyan Rugar Gagare-Musaiwa, da ke a yakin Karanka ta Karamar hukumar Birniwa a Jihar Jigawa kame da cin wuta. ko da shike ba a gane ba da sanadiyar kamewar wutan, amma mun gane a

Naija News Hausa da cewa gonar hatsin na da girman gaske, kuma a kilan hatsi da ta kone zai fi kamanin kudi na Naira Miliyan Daya.

An gabatar da kamun wutan ne ga manema labaran tarayya (NAN) daga bakin kakakin yada yawun karamar hukumar, Alhaji Abdullahi Yakubu.

Malam Yakubu ya bayyana da cewa gonar da ta kone ta kumshi ajiyar Gero, Dawa da sesame. Kuma gonar ta kame da wuta ne misalin karfe biyar 5 ta maraicen ranar Asabar da ta gabata.

“Bamu gane ko menene ya kawo sanadiyar kamewar wutan ba har yanzu” inji Yakubu.

“An tsarafa Gonan ajiyar hatsin ne don ajiye samar da abinci a gaba”
Ya kara da cewa, kansilan da ke wakiltar karamar hukumar, Alhaji Garba Kabewa ya ziyarci wajen, kuma ya gabatar da bakin cikin sa ga wannan abin da ya faru ga wadanda ke da gonar.

Yakubu, ya bukaci hukumar yankin da bada gudumuwa ga wadanda ke da gonar da ta kame da wuta don rage masu matsalar yunwa.

Mai anguwar kauyan Musaiwa, Alhaji Garba Mohammad ya gabatar da cewa abin mamaki ne ganin yadda gonar ta kame da wuta, kuma ya bayyana nasa gaisuwar tausayi ga masu gonar.

Karanta wannan kuma: Shugaba Muhammadu Buhari da Matarsa, Aisha Buhari a mazaba

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.