Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli yadda Shugabanci ta yi wa Sanata Bukola Sarki Ba’a don ya fadi zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugabancin kasar Najeriya sun yi wa Saraki Ba’a ga faduwar zaben ranar Asabar.

Ayayin da aka sanar da sakamakon zaben Gidan Majalisa jiya, Lahadi 24 ga Watana Fabrairu bayan gwagwarmayan zaben ranar Asabar da ta gabata, Shugabancin kasar sun yi wa Bukola Saraki, shugaban sanatocin Najeriya ba’a a yayin da suka gane da cewa dan takaran ya fadi ga zaben kananan hukumomi hudu da ke a Jihar Kwara.

Kamar yadda Naija News ta sanar a ranar Lahadi da cewa dan takaran Jam’iyyar APC ga gidan Majalisar Dattijai a Jihar Kwara, Dakta Yahaya Oloriegbe ya lashe zaben gidan majalisar dattijai da kuri’u fiye da Sanata Bukola Saraki.

Rahoto ta bayar da cewa dan takaran Gidan majalisar dattijai na Jam’iyyar APC, Oloriegbe ya samu kuri’u kimanin 123, 808, shi kuma sanata Bukola Saraki ya samu kuri’u 68, 994 a kananan hukumomin hudu ta Jihar Kwara ga zaben Gidan Majalisan Dattijai.

Ma’aikacin shugaban kasa, Bashir Ahmad da ganin sakamakon kuri’un gidan majalisar Jihar, sai ya aika sakon tayin murna ga dan takaran Jam’iyyar APC ga zaben gidan majalisar Kwara, Yahaya Oloriegbe a layin yanar gizon nishadi ta twitter.

Ya kuma nuno wata hoto da ke dauke da shugaba Muhammadu Buhari da Oloriegbe.

“Ó tó gé! Barka da cin nasarar zabe, Sabon sanata, Yahaya Oloriegbe” wannan shi ne sakon Bashir.

Karanta wannan kuma: Kalli yadda dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da matarsa, Titi suka jefa kuri’ar su a ranar Asabar