Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 25 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 25 ga Watan Fabrairun, 2019

1. Hukumar INEC ta gane da kashe wani malamin zabe a Jihar Rivers

Shugaban Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu ya gabatar da cewa an kashe wani malamin zabe a wata mazaba ta Jihar Rivers a zaben ranar Asabar da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da sanarwan shugaban ne a yayin da yake gabatarwa da manema labarai a gidan tattaunawa ta birnin tarayya, Abuja a ranar Lahadi da ta gabata.

2. Wuta ta kame Ofishin Hukumar INEC a Jihar Osun

Wata Ofishin hukumar zaben kasa (INEC) da ke a yankin Ijebu-Ijesha ta karamar hukumar Oriade a Jihar Osun ta kame da wuta.

Rahoto ta bayar da cewa Ofishin ya kame da wuta ne misalin karfe 3:00 na safiyar ranar Lahadi da ta gabata.

3. Jam’iyyar APC sun bukaci kame Buba Galadima

Jam’iyyar APC sun sanar da cewa a kame Buba Galadima, jigon Jam’iyyar PDP akan laifin furcin da yayi na cewa a gabatar da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin mai nasara ga zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Jam’iyyar APC sun gabatar da hakan ne ganin wata bidiyo da Galadima ya tsarafa, inda ya nuna kansa kamar shine ne kakakin Jam’iyyar PDP a cikin bayanin sa.

4. INEC ta daga sanar da sakamakon zaben ranar Asabar

Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta daga sanar da rahoton zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar zuwa karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu ya gabatar da hakan ne a ranar Lahadi bayan sanar da bude gidan kirgan zabe.

5. Hukumar EFCC ta halarci gidan kirgan zaben Jihar Legas

Hukumar Bincike da Hukunci akan Tattalin Arzikin kasa, EFCC sun fadawa gidan kirgan zabe ta Jihar Legas.

Mun gane a Naija News Hausa da cewa hukumar sun fadawa gidan kirgan zaben ne da ke a yankin Yaba ta Jihar Legas don gudanar da bincike.

6. ‘Yan ta’adda sun kashe jami’an Sojojin Najeriya a ranar zabe

Kimanin mutane bakwai hade da sojojin Najeriya suka rasa rayukan su a lokacin da ‘yan hari da bindiga suka fada wa yankin Abonnema, da ke a karamar hukumar Akuku Toru ta Jihar Rivers.

Naija News ta samun tabbacin mutuwar mutanen ne a bayan da sojojin Najeriya da ke yankin suka yi ganawar wuta da ‘yan hari da bindigar a ranar Asabar da ta wuce.

7. Mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo ya fadi ga kuri’u a mazaban sa

Jam’iyyar PDP ta mazaban VGC (Victoria Garden City) a Jihar Legas ta lashe zaben shugaban kasa da ta Gidan Majalisai da kuri’u fiye da Jam’iyyar APC.

Naija News ta gane da cewa a nan mazaban ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jefa nasa kuri’ar ga zaben shugaban kasa ta ranar Asabar.

8. Atiku bai samu zabe ko daya ba a mazaban Oshiomhole

Adams Oshiomhole, Ciyaman na Jam’iyyar APC ta tarayya ya lashe zaben mazaban sa ga zaben shugaban kasa.

Mun gana a Naija News da cewa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bai samu kuri’a kod guda ba a mazaban Adams Oshiomhole a Jihar Edo ga zaben ranar Asabar da ta gabata.

9. Ina da tabbacin lashe zaben shugaban kasa – inji Fela Durotoye

Dan takaran shugaba kasa na Jam’iyyar ‘Alliance for New Nigeria’ (ANN), Fela Durotoye, ya bayyana da cewa yana da bugun gaba da cewa zai lashe zaben shugaban kasa ta ranar Asabar da aka yi.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Fela Durotoye na daya daga cikin manyan ‘yan takaran shugaban kasa ta tseren zaben shekarar 2019.

Ka sami karin labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa