Connect with us

Uncategorized

Sanata Dino Melaye ya lashe zaben kujerar Sanata a Jihar Kogi ta Yamma

 

Sanatan Jihar Kogi ta Yamma da jami’an ‘yan sandan Najeriya suka tsare gidan sa da tsawon kwanaki, Dino Melaye ya lashe zaben kujerar gidan majalisar wakilai ta Jihar Kogi ta Yamma.

Dan takaran Sanatan daga Jam’iyyar PDP ya lashe zaben ne da kuri’u 85,395, fiye da dan adawan takaran sa daga Jam’iyyar APC, Smart Adeyemi mai kuri’u 66,901.

An gabatar da wannan ne daga bakin malamin zaben jihar da ke shugabancin mayar da sakamakon zabe a birnin tarayya, Emmanuel Bala.

Naija News Hausa na da sani cewa Sanata Dino Melaye ya janye ne daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP ‘yan lokatai kadan da ya gabata kamin aka fara hidimar zaben shekarar 2019.

“Godiya ga Allah sarkin sarakuna, har abada. An sanar da ni a matsayin dan takara da ya lashe zaben sanatan yanki na, Allah kawai ke iya wannan, Godiya gareshi har abada. Mutanen Jihar Kogi ta Yamma, na gode maku kwarai da gaske” wannan itace sakon sanata Dino Melaye bayan da hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben kujerar sanatan yankin.

 

Karanta wannan kuma: Kalli yadda shugaba Muhammadu Buhari ya leki takardan zaben matarsa, Aisha Buhari

Advertisement
close button