Connect with us

Uncategorized

2019: Bamu amince da rahoton zaben shugaban kasa ba – inji Jam’iyyar PDP ta Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jam’iyyar PDP ta Jihar Kano sun bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaben shugaban kasa ta bana

A yayin da hukumar INEC suka sanar da sakamakon kuri’ar zaben shugaban kasa ta Jihar Kano, Jam’iyyar PDP sun bayyana rashin amincewar su da rahoton zaben da cewa akwai alamar makirci.

Rabiu Sulaiman Bichi, da ke wakilcin jam’iyyar PDP a Jihar ya bayyana da cewa bai yadda da rahoton ba a yayin da ya gane da cewa an canza lambobin kuri’un.

“Ba zamu amince da irin wannan sakamakon ba kuma zamu dage da hakan, zamu koma da bincike akan wannan kamin mu san matakin da zamu dauka” inji Rabiu.

“mun gane da cewa mai jagoran hidimar zaben jihar ya gabatar da cewa ba a yi amfani da na’urar binciken katin zabe ba ga zaben shugaban kasa da ta gidan majalisa, sa’anan hade da kuri’u fiye da lamban jam’ar da aka amince da su ga jefa zabe” inji shi.

Karanta wannan kuma: Kalli yada shahararrun ‘yan shirin fim na Kannywood suka jefa kuri’ar su