Uncategorized
Atiku ya sha da kyar a Jihar Taraba, kalli sakamakon kuri’un

Dan takara shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha da kyar ga kuri’ar Jihar Taraba.
Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) sun gabatar da rahoton zaben shugaban kasa na Jihar Tarabar. Sakamakon zaben jihar ya nuna yadda dan takaran, Atiku ya sha da kyar da ‘yan kuri’u kadan fiye da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC, shugaba Muhammadu Buhari.
Ga sakamakon kuri’un Jihar a kasa, kamar yadda hukumar INEC suka sanar;
Jam’iyyar APC na da kuri’u 324,906
Jam’iyyar PDP kuma na da kuri’u 374,743
Rahoton ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fadi da kuri’u 49,837.
Sauran jihohi zasu biyo a baya. Ka diba shafin Naija News Hausa a kowane lokaci don samun cikakken bayani game da sakamakon zaben shugaban kasa.
Continue Reading