Connect with us

Labaran Najeriya

Ya Wazirin Adamawa, Ka kira Buhari da yi masa Barka – inji Dele Momodu

Published

on

Sananen Maikudi, Mallami, Mai Gidan Jaridan Ovation, dan siyasa da masana’ancin kasar Najeriya, Dele Momodu ya aika wata sako a yanar gizon nishadarwa ta twitter.

A yayin da Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa, INEC ke gabatar da rahotannin kuri’un Jihohin kasar na zaben shugaban kasa, Dele Momodu a kulawarsa na ganin cewa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC, shugaba Muhammadu Buhari na da kuri’u fiye da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sai ya wallafa wannan sakon.

“Ya Wazirin Adamawa, a matsayin ka na mai bi da ganewa, na san ka bada gaskiya da cewa Allah ne kawai mai bada nasara ya kuma dauke daga duk wanda ya gan dama. Na shawarce ka, kada ga yi jinkiri, ka aika sakon barka ga dan Muhammadu Buhari. Na tabbata akwai ribar da zaka samu daga hakan”.

Ga sakon a kasa kamar yadda ya aika a turance;

Ko da shike mutane sun mayar da martani ga wannan da cewa ba daidai bane Atiku ya amince da sakamakon zaben ganin cewa an hada da makirci kwarai da gaske.

Ga kadan daga cikin sakonnan ‘yan Najeriya game da zancen;

Mun ruwaito a baya da cewa hukumar gudanar da zaben kasa, INEC sun yi barazanar cewa ba zasu raunana amincin su ba ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019