Labaran Najeriya
Zaben2019: Shugaba Buhari ya ziyarci dakin kirgan zabe, ya kuma leka rahoton kuri’u
A yayin da Hukumar gudanar da zaben kasa ke hadawa da sanar da sakamakon kuri’un jihohi, shugaba Muhammadu Buhari yayi wa dakin kirgan zaben ziyarci ban mamaki.
Mun gane a Naija News Hausa da cewa shugaban ya ziyarci dakin kirgan zaben ne don leka yadda suuke gudanar da kirgan, da kuma gane sakamakon kuri’u.
Mun gane da wannan ne a yayin da Mai yada labarai ga yanar gizo na shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya gabatar a layin yanar gizon nishadi da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci dakin kirgan zabe don gode masu da yadda suke tafiyar da aikin su.
Mun tuna a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fada da cewa ba watakila, shi ne zai lashe zaben 2019. Shugaban ya fadi hakan ne a yayin da yake mayar da martani ga tambayar da manema labaran BBC Hausa suka yi wa shugaban a lokacin da zai bar runfar zaben sa a Daura.
Tambayar na kamar haka, daga bakin manema labaran;
“Ranka shi dade shugaba, shin zaka aika gaisuwar murna ko kira ga duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa ta 2019?
“Ba wata wai-wai, zan taya kaina murna don ni zan lashe zaben” inji shugaba Muhammadu Buhari.
Mun kuma tuna da cewa shugaban ya fada da cewa ba zai yi magana ko wata furci akan rahoton zaben ba, sai har hukumar gudanar da zaben kasa sun sanar da rahoton zaben.