Uncategorized
An ribato Malam Nazifi da konewar wuta a Jihar Kano
Hukumar Kashe Kamun Wuta (Fire Service) ta Jihar Kano sun ribato ran wani daga konewar wuta
Wani mutum mai suna Malam Nazifi Abdullahi, a daren ranar Talata da ta gabata ya tsira daga konewar wuta a gidansa da ke a Sharada Phase I ta Jihar Kano, a yayin da hukumar kashe kamun wuta suka taimaka wajen ganin cewa bai kone da wutar ba.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Dakin kwanan ‘yan Makarantar Jami’ar Wudil da ke a Kano ya kame da wuta.
Kakakin yada yawun hukumar, Saidu Mohammed ya bayyana da cewa wutar ta kama ne da Malam Nazifi a cikin gidan sa kamin suka taimaka wajen ribato ransa.
“Wuta ya haska ne da gidan mutumin mai shekaru da 45 a yayin da yake cikin gidan sa” inji Saidu.
“Mun taimaka ne da ribato ran mutumin bayan da muka samu kirar gaggawa misalin karfe 8:10 na maraicen ranar Talata daga bakin wani mazaunin anguwar, Malam Auwalu Abdullahi.
Malam Saidu ya kara da cewa sun aika da ma’aikatan hukumar ne a gaggauce don kashe wutan da kuma ribato ran Malam Nazifi bayan da suka karbi kira daga Auwalu game da kamun wutar.
“Dakin dafa abinci da ke cikin gidan ya kame da wuta, mutumin kuma ya ji ciwo da dama, amma a halin yanzu yana can Asibitin Aminu Kano don karban kulawa ta gaske”.
Ya kuma bayyana da cewa gidan ta kame ne da wuta sanadiyar Na’urar girki na Gas, da aka fi sani da ‘Cooking Gas’.