Connect with us

Uncategorized

An sace mutane 35 a Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta samu rahoto da cewa wasu ‘yan hari sun sace kimanin mutane 35 a Jihar Neja

“Mahara da bindigan sun fado wa kauyan mu ne a tsakiyar rana da harbe-harben bindiga a sama, bamu da wata mafita iya fadawa cikin daji” inji Shuaibu, wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da aka yi wa harin a karamar hukumar Shiroro.

Rahoto ta bayar da cewa kimanin mutane Talatin da biyar (35) ne aka sace a yankin, bayan mutane biyar (5) da aka kashe a nan take. kamar yadda muka samu rahoton.

Mugun harin ya faru ne ‘yan kwanaki da suka gabata a cikin yankuna goma sha bakwai (17) da ke tsakanin karamar hukumar Rafi da kuma Shiroro ta Jihar Neja.

“Iyalan wasu daga cikin mutanen da aka sace sun rigaya sun biya kudi don samun kubutar da mutanen su daga hannun ‘yan harin. Wasu lokatai ma mu kan je neman kudi ne don mu samu ribato ran wadanda ‘yan hari ke sace wa a yankunan mu” inji Aliyu Shuaibu.

Aliyu Shuaibu ya bayyana ga manema labarai a ranar Talata da ta gabata da cewa sun iya gane cewa ‘yan harin makiyayan shanaye ne da tumaki. “Kuma sun gane da sace-sacen mutane a yankin mu, amma a wannan lokaci gaskiya sun sace mutanen mu da yawar gaske” inji shi.

“Sun sace Mata, Mazaje, yaran mu da kayakin mu duka” inji Hafsat Ibrahim, daya daga cikin mazaunin yankin Shiroro. inda abin ya faru.

Hassan Garba, daya daga cikin mutanen da aka sace a baya, ya fada da cewa “Sun sace ni ne da ‘yan uwa na, suka kuma bukace mu da biyar naira Miliyan goma shadaya (11) kamin su sake mu”

“Sun sake ni ne don inje neman kudi in kuma dawo ron ribato ran ‘yan uwa na. Duk iya kokari na, Miliyan daya ne kawai na samu. da kuma na biya Miliyan daya din, sai ko suka sake ni da ‘yan uwa na duka” inji Hassan.

“Da ace ban biya kudin ba, da sun kashe mu duka” inji shi.

Gwamnan Jihar, Abubakar Belllo, yayi rantsuwa da cewa zai magance wadanda ke aiwatar da irin wannan mugun halin.

Ya kuma gabatar da cewa gwamnatin jihar ta fara daukar matakai akan hakan don ganin cewa an samar da isashen tsaro a jihar.

Gwamna Bello ya gabatar da hakan ne a lokacin da ya ziyarci mutane 4,600 da ‘yan harin suka sake bayan kame su a Kagara a wata makarantar Firamare ta Pandogari.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa jami’an tsaron jihar Neja sun kame wata mai suna Habiba Usman da ake zargi da sanadiyar kamewan da ‘yan hari suka yi mata.