Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 27 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 27 ga Watan Fabrairun, 2019
1. Hukumar INEC ta gabatar da Buhari mai nasara ga zaben shugaban kasa ta 2019
A jiya, Laraba 26 ga watan Fabrairu, Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa, INEC ta gabatar da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
Mun gane a Naija News Hausa da cewa hukumar sun gabatar da sakamakon jimlar zaben shugaban kasa ne daga bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu, 2019 a misalin karfe 4:39 na safiya. Bayan an gane a karshen sakamakon da cewa Buhari ya fiye dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuri’u.
2. Atiku ba zai amince da nasarar Buhari ba – inji Jam’iyyar PDP
Jam’iyyar PDP sun yi barazanar cewa dan takaran su ga tseren shugaban kasa, Atiku Abubakar ba zai amince da gabatar da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari ba a matsayin mai nasara ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
Muna da sani a Naija News da cewa hukumar INEC ta gabatar da sakamakon zaben ne a daren ranar Laraba da ta gabata.
3. Shugaba Muhammadu Buhari yayi ganawa da El-Rufai a fadar shugaban kasa
A ranar Talata da ta gabatar, shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawa da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a fadar shugaban kasa.
Mun samu tabbacin hakan ne a Naija News Hausa a yadda shugaban ya bayyana a shagin yanar gizon nishadarwa ta shugaban, na twitter @NGRPresident. Mun kuma gane da cewa sun yi ganawar ne don tattauna matsalar tsaro a Jihar Kaduna.
4. PDP: Har yanzu ba a gane da inda Buba Galadima yake ba
Harwayau ba a gane da wajen da Buba Galadima, jigon Jam’iyyar PDP da ke zargin shugaba Muhammadu Buhari yake ba.
Hukumar Bincike ta Jihohi (DSS), Jami’an tsaron ‘yan sanda da Rundunar sojojin kasa sun bayyana da cewa Buba Galadima bai a wajen su.
Naija News Hausa ta gane da cewa an sace buba Galadima ne rana ta biyu bayan zaben shugaban kasa da ta gidan majalisai da aka yi ranar Asabar da ta gabata.
5. Mutane da yawa sun rasa rayukan su a Jihar Kaduna
A sakamakon wata sabuwar hari da ‘yan hari da bindiga suka kai a karamar hukumar Kajuru da ke a Jihar Kaduna, mutane da dama suka rasa rayukan su.
Rahoto ta bayar da cewa mutanen da su ka mutu sun kasance ne daga kauyan Karmai da ke a yankin Maro a karamar hukumar Kajuru.
6. Tinubu ya mayar da martani game da rashin amincewar Jam’iyyar PDP
Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, ya mayar da martani game da zancen rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da ta gidan Majalisai na shekarar 2019.
“duk wanda bai amince da sakamakon zaben ba, lallai ba dan siyasa bane” inji shi.
7. Sanata Bukola Saraki ya gabatar da gaisuwa ga mai nasara ga tseren dan Majalisar Kwara
Shugaba Sanatocin kasar Najeriya, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya bayyana da cewa duk da makirci da yadda aka gudanar da hidimar zaben gidan majalisa ta ranar Asabar da ta gabata, ya taya ‘yan takara da suka lashe zaben da murna.
Naija News ta gane da hakan ne kamar yadda Saraki ya gabatar da sanarwan ta wurin mai bada shawara ga sanatan ga lamarin labarai, Yusuph Olaniyonu a ranar Talata da ta gabata.
Ya bayyana da cewa duk da cewa ba a yi amfani da na’urar binciken katin zabe ba a kashi 70% na Jihar da kuma wasu zargi na makirci ga zaben, ya taya dan adawan sa da murna ga lashe zaben.
8. Kunyar Jam’iyoyin kasa (CUPP) sun ki amince da rahoton zaben shugaban kasa
Bayan da hukumar INEC suka gabatar da sakamakon rahoton zaben shugaban kasa da ta gidan majalisai, kungiyar jam’iyoyin siyasan kasar Najeriya (CUPP) sun bukaci cewa a hana hukumar INEC, da ‘yan jam’iyyar APC da fita kasar Najeriya zuwa kasar waje.
Hukumar sun gabatar da hakan ne daga bakin kakakin yada yawun kungiyar, Mista Imo Ugochinyere a wata sanarwa ta ranar Litinin da ta gabata.
Ka samu cikakken labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa