Uncategorized
Zaben 2019: Buba Galadima da aka sace ya aika sako a gidansa

Jigon Jam’iyyar PDP, Alhaji Buba Galadima da aka sanar da cewa an sace ranar Lahadi bayan zaben shugaban kasa ta ranar Asabar da ta gabata, ya aika wata sako a gidansa.
Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Galadima daman mamba ne da kuma shugaba a Jam’iyyar APC kamin janyewarshi zuwa Jam’iyyar PDP a yayin da ake batun hidimar zaben 2019.
Rahoto ta bayar a baya da cewa wasu ‘yan hari da ba a san da su ba sun sace Alhaji Buba Galadima ne a gidan sa nan birnin Abuja ranar Lahadi, 24 ga Watan Fabrairu, ‘yan awowi kadan bayan da aka kamala zaben shugaban kasa da ta gidan majalisai.
Tun a wannan lokacin kuma babu wanda ya samu sanin ko ina ne Galadima ya ke. Amma da safiyar yau Laraba, 27 ga Watan Fabrairu 2019, Iyalin Galadima sun bayyana da cewa sun samu wata wasika daga wajen Galadima, kuma ya tabbatar masu da cewa yana cikin koshin lafiya.
“Ko da shike bai bayyana mana ko ina ne yake ba, amma ya sanar a cikin wasikar da cewa yana cikin kwanciyar hankali” inji matarsa, Hajiya Fanna Galadima, a yayin da ta ke gabatar da hakan ga manema labarai.
“Mun karbi sakon ne a hannun wani da bamu gane da shi ba a nan gidan mu da ke Wuse II, anan Birnin Abuja” inji Dakta Shettima Galadima, yaron Alhaji Buba Galadima.
Hajiya Fanna ta karasa da bayyana yadda aka sace mijin ta. Ta ce “Mun gano wata mota ne da ke zagayar hanyar gidan mu kamin dada ya fake kusa da kofar gidan mu”
“Ba da dadewa ba, maigidana ya fita daga gidan. jim kadan kawai sai muka samu labari da cewa an sace maigidana” inji ta.
“Duk da cewa ya bayyana mana a cikin sakon da cewa yana cikin koshin lafiya, mu dai hankalin mu bai kwanta ba” inji Hajiya Fanna.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Buba Galadima na zargin cewa an bada naira Miliyan 45 ga yankuna don ‘sayen hankalin mutane ga fitar ralin Buhari