Labaran Najeriya
Kalli yada wani ya taya shugaba Muhammadu Buhari murna a Jihar Bauchi
Mun karbi wata rahoto a Naija News Hausa yadda mutanen Jihar Bauchi suka nuna murnan su ga shugaba Muhammadu Buhari ga lashe zaben shugaban kasa na 2019.
Mun ruwaito a baya da cewa an gabatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben shugaban kasa ta tseren takaran shekarar 2019.
Ga hoton wani matashi a kasa daga jihar Bauchi da ya nuna irin tashi murna da cin nasaran shugaba Buhari. An gano matashi da yatsun sa hudu (4) a sama, watau alamun cewa shugaban zai sake mulkin shekaru hudu. An kuma gano matashin yadda ya tsoma kansa a cikin kwata a sunan murna ga cin nasaran Buhari.
Ka tuna da cewa hukumar gudanar da zaben kasa a ranar jiya sun ba wa Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo takardan sake komawa ga mulki.
An gabatar da hakan ne bayan da hukumar suka gane da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya lashe tseren da kuri’u 15,191,847, fiye da sauran yan takara; hade da dan adawan sa, Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran jam’iyyar PDP.