Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 28 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 28 ga Watan Fabrairun, 2019

1. Buhari da Osinbajo sun karbi takardan komawa ga kujerar mulkin kasa

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo,  a ranar Laraba da ta gabata sun karbi takardan sake komawa ga kujerar shugabancin kasar Najeriya na karin tsawon shekaru hudu.

Mun gane da hakan ne a Naija News Hausa a yayin da shugaban hukumar zaben kasa, INEC ta mika masu takardan a nan birnin tarayya, Abuja, ranar 27 ga watan Fabrairu, 2019.

2. Mun bizne Saraki a lamarin siyasa – inji Adams Oshiomhole

Ciyaman na Jam’iyyar APC na  tarayya, Adams Oshiomole ya furta da cewa jam’iyyar su ta bizne shugaban sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki daga lamarin siyasar kasar.

Naija News ta gane da cewa, shugaban hidimar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Saraki ya fadi ga zaben kujerar gidan majalisar tarayya daga Jihar Kwara bisa sakamakon rahoton zaben gidan majalisai da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

3. Bola Tinubu ya bayyana abin da Muhammadu Buhari zai yi a karo na biyu ga mulkin kasa

Shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana da cewa zaben tseren shugaban kasa ta bana ta kasance da rashin makirci ko kadan, kuma zaben ta baiwa daman ra’ayi ga al’ummar kasar Najeriya.

Tinubu, a cikin bayanin sa lokacin da yake aika sakon barka ga shugaba Muhammadu Buhari, ya ce “Al’ummar kasan Najeriya sun bada dama ga shugaba Buhari don sake mulkin kasar ga tsawon shekaru 4. wannan kyakyawar abu ne, kuma ina tabbatar da cewa shugaban zai kafa zamantakewar lafiya, tsaro ta kwarai da kuma dade hanyoyin cin hanci  da rashawa a kasar” inji shi.

4. Kada ka je Kotu – Agbakoba ya shawarci Atiku

Babban mamban kungiyar Manyan masu bada shawara ga kasa (NAN), Sarki Olisa Agbakoba ya shawarci dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Atiku Abubakar, da cewa ya manta da batun kai kara sakamakon zabe a kotu.

“Duk da cewa na gane zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 ya karshe ne da makirci, amma ina mai shawara kada ka yi kara akan hakan, don kare mutuncin ka” inji Agbakoba.

5. Wata rukuni ta bukaci Hukumar INEC da bayyana dalilin da ya sa suka soke kuri’u kimamin Miliyan daya

Wata rukunin Ma’aikatan Najeriya da suka dauki dama ga zaben shugaban kasa ta 2019 sun yi kirar kula ga hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), da cewa ta bayyana dalilin da yasa hukumar ta soke kuri’u kusan fiye da Miliyan daya.

Mun tuna a Naija News Hausa da cewa Jam’iyyar PDP sun fada da cewa ba zasu amince da sakamakon rahoton zaben shugaban kasa da ta gidan majalisai ba.

6. Atiku ya bayyana dalilin da ya sa ba zai taya shugaba Buhari murna ba ga lashe zabe

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ga tseren zaben 2019 da aka gama, Atiku Abubakar, ya nuna godiyan sa da murna ga ‘yan Najeriya duka da irin goyon baya da aka nuna masa duka na jefa masa kuri’u ga zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

A cikin bayanin sa, ya gabatar da zargin cewa jam’iyyar APC sun nuna makirci ga zaben 2019 don taimaka ga dan takaran su ga lashe zaben.

7. Ba ku san komai ba -inji Gwamna Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya mayar da martani game da zancen kuri’un Jihar Kano. Gwamnan, a yau Alhamis a ziyarar da ya kai ga fadar shugaban kasa, ya furta da cewa masu zargi, da jita-jita game da zaben 2019 basu san abin da suke yi fadi ba.

Muna da sani a Naija News da cewa Kano na daya daga cikin jihohin kasar da suka jefa wa shugaba Buhari kuri’u mai yawan gaske.

8. Wata yarinya ta fashe da kuka wajen taya Buhari murna da nasarar zabe

Da safiyar nan, Naija News Hausa ta gano bidiyon wata ‘yar mace da ta fashe da hawayen murna a yayin da take bayyana irin murna da farin cikin cewa shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo sun lashe tseren zaben shekarar 2019.

‘Yar yarinyar ta wallafa bidiyon kanta, yadda ta ke murna da cewa Allah ya sake mayar da shugaba Muhammadu Buhari a kan kujerar mulki.

Karanta cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa