'Yan Hari da bindiga sun kai sabuwar hari a Jihar Zamfara | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

‘Yan Hari da bindiga sun kai sabuwar hari a Jihar Zamfara

Published

Mahara da bindiga sun sake kai wata sabuwar farmaki a wata kauyan Jihar Zamfara da ake kira Anka.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Jihar Zamfara na daya daga cikin Jihohin da ‘yan hari da bindiga da masu sace-sace mutane ke aiwatar da mumunar hari. Duk da irin kokari da barazanar da hukumomin tsaron kasar ke yi, ‘yan ta’addan basu daina aiwatar da ayukan su ba.

An bayyana kamar yadda muka samu rahoto da cewa ‘yan harin sun fada wa mutanen Kawaya ne da ke a kauyan Anka ta Jihar Zamfara, inda suka lallace gidajen mutane, da motoci, harma da baburan su.

Abin takaici, mutane goma sha ukku suka rasa rayukansu sakamakon harin.

Wannan abin ya faru ne yau Alhamis, 28 ga Watan Fabrairu, 2019. Rana da ke biye da nasarar shugaba Muhammadu Buhari da lashe zaben kujerar shugabancin kasar Najeriya.

Mun tuna da cewa Buhari a cikin gabatarwa da yayi a ranar Laraba da ta gabata, ya ambaci karfafa tsaro a jihohin kasar a cikin mulkin sa. Ya kuma tabbatar da cewa za a dauki matakai ta musanman don magance ta’addanci da kashe-kashe a kasar.

Karanta wannan kuma: Jigon Jam’iyyar PDP, Buba Galadima da ‘yan hari suka sace ya wallafa wasika zuwa ga Iyalin sa

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.