Connect with us

Uncategorized

Zaben 2019: Karanta abin da Atiku ya fada game da zaben ranar Asabar

 

Alhaji Atiku Abubakar, a bayanin sa a ranar Laraba da ta gabata game da batun zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar da ta wuce; ya ambaci wasu abubuwa na kulawa guda takwas.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Atiku yayi kirar gaggawa ga ‘yan Jam’iyyar PDP a lokacin da hukumar gudanar da zaben kasa ta sanar da rahoton zaben shugaban kasa ranar Laraba. Dan takaran ya kuma bayyana da cewa bai amince da sakamakon zaben ba.

A bayanin Atiku wajen zaman tattaunawa da suka yi a birnin Abuja, ya bayyana a fili ga jama’a da cewa bai amince da rahoton da hukumar INEC ta gabatar da ita ba, da cewa rahoton bai nuna ra’ayin mutane ba.

Mun gane da cewa shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya gabatar bayan da suka gama lissafin sakamakon zaben da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’u 15,191,847, shi kuma Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u 11,262,978. Ya kuma gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga tseren takaran kujerar shugaban kasa.

Ga kadan daga cikin bayanin Atiku Abubakar a kasa;

Da farko dai ya nuna farin cikin shi ga irin goyon baya da al’ummar Najeriya suka bashi wajen fitowa da yawar su don jefa masa kuri’un su, duk da irin matsalar tsaro da ke kasan.

Bayan hakan sai yace;

1. Ya kamata ne ace Dimokradiyya ya bayyana ra’ayin mutane, amma hakan bai kasance ba ga zaben ranar Asabar da ta gabata.

2. Akwai kanancin samar da katunan zabe a yankuna da jihohin da Jam’iyyar PDP ke da karfi

3. An samu karin yawar rajistan katin zabe da kuma karban  katunan zabe a yankuna da Jam’iyyar APC  ke da karfi.

4. Yawar kuri’un Jam’iyyar PDP a Jihohin Kudu maso gabas da kuma ta Kudu maso kudu bai kasance da fiyewa ta kwarai ba.

5. Adadin sakamakon kuri’u da hukumar INEC ta gabatar ba daidai ba ne ga zaben ranar Asabar, 23 ga wata Fabrairu, ta shekarar 2019.

6. Ba wai ina magana a matsayin mamban Jam’iyyar PDP ko kuma dan siyasa ba ne, amma ina magana a matsayina na dan Najeriya.

7. Ni, Atiku Abubakar, ban amince da sakamakon rahoton zabe da hukumar INEC ta gabatar da shi ba, da kuma sanar da Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben shugaban kasa ba.

8. Duk wanda ya gane da wannan kuma ya raunana da hakan ya kwantar da hankalin shi, zamu dauki mataki ta musanman akan haka.

 

Advertisement
close button