Connect with us

Uncategorized

Published

on

Jami’an ‘yan sandan Jihar Neja sun kame Mohammed Manu da ya kashe matarsa wai don ta hana shi Jima’i

Wani mai mutumi mai shekaru 35 da haifuwa ya kashe matarshi da ake kira Bulo, wai don ta hana shi yin jima’i da ita.

Ko da shike mutumin ya bayyana da cewa sau da dama ya yiwa matar kashedi da kuma bayyana mata da cewa “Haram ce mace ta hana mijin ta da yin jima’i da ita”.

Naija News ta gane da cewa akwai yara biyar tsakanin mutumin da matar kamin ya kashe ta.

“Na harbe ta ne da bindiga bayan da na gan abin nata ya yi min yawa. kullum sai kokarin hana ni jima’i da ita, ta dauke ni kamar kuturu” inji Manu.

“Jima’i abu ne mai muhinmanci kwarai da gaske a cikin aure, a koyaushe da na bukaci matana da hakan, sai ta hana ni. ta kan dauke ni ne kaman kuturu, ni kuma ban amince da wannan ba”

“A ranar, na bukace ta da jima’i sai ta ki’, da na matsa mata kuma sai ta ture ni kasa. Ni kuma sai na fusata har na rasa hankali na. daga nan sai na dauki bindiga na harbe ta” inji Manu.

A halin yanzu, Ofishin jami’an tsaro ta yankin New Bussa sun mika karar Mohammed Manu a Kotun kara.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa wani mutumi ya yi wa matarsa duka akan cewa bata gayar da kishiyar ta ba a cikin kasuwa.