Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Wani ya rasa aikin tukin mota wai don ya taya Buhari murna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani mutumin mai suna Omo Oshodi, ya bayyana a shafin yanar gizon nishadarwa ta twitter, da cewa ya rasa aikin sa don ya nuna murnan sa ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari ga tseren takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019.

“Na rasa aikin tukin mota na a yau. Maigida na ya tsige ni daga aiki don ya ji lokacin da ni ke hirar murna shugaba Muhammadu Buhari da wani abokin aiki na a wajen. ban taba zaton cewa wani mutum zai iya kasance da rashin mutunci ba kamar haka” inji shi.

“Na bada gaskiya da cewa Allah ba zai rabu da ni da iyali na ba. zai kuma taimaka mani da wata aiki” inji Omo Oshodi.

Ga bayanin shi a kasa a layin twitter;

Karanta bayanin mutane a kasa game da labarin;

https://twitter.com/themangerajake/status/1101175271770767360

Kalli yadda Omo Oshodi ya mayar da martani ga fadin wani;