Connect with us

Uncategorized

An kame Mista Emmanuel da ya kashe yaron shi da du’ka

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an ‘yan sandan Jihar Rivers sun kame wani mai shekaru 40 da haifuwa da ya kashe yaron shi sakamakon mugun duka.

Rahoto ta bayar da cewa mutumin, Mista Israel Emmanuel Okon ya yi wa yaron duka ne wai don yaron ya ci abin da aka ajiye masa.

Mista Austin Agbonlahor, Kwamishanan jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Rivers, a bayanin shi da manema labarai ya bayyana da cewa sun kame mista Israel Emmanuel Okon ne da zargin kashe yaron da ya haifa sakamakon mugun duka da ya yi wa yaron a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2019.

“Mun kame Emmanuel ne da laifin kisan kai. Ya kashe yaron shi da duka wai don yaron ya canye masa abinci” inji Mista Austin.

Naija News Hausa ta gane da cewa Mista Emmanuel ne yayi karan kanshi ga jami’an tsaro bayan da ya gane da cewa yaron ya mutu sakamakon duka. kamar yadda ya bayyana ga ofishin ‘yan sandan jihar.

Mista Israel Emmanuel Okon, mazauni ne na Obio Inwang, wata kauye da ke a karamar hukumar Akamkpa ta Jihar Rivers.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hakilu Saidu, wani manomi mai shekaru 30 da ke zama a wata kauye mai suna Yankara, a karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina ya kashe wata diyar agolan makwabcin sa da ke da shekaru hudu 4.

Kwamishanan ‘yan sandan, Mista Agbonlahor ya kara da cewa mutumin ya riga ya amince da laifin sa kuma zamu yi karar shi a kotu don hukunci.

An bayyana da cewa Mista Emmanuel ya roki jami’an da su sake shi don ya samu damar kula da sauran yaran sa biyar tun da uwarsu bata saura tare da shi ba.

“Ban sa ran cewa yaron zai mutu ba ko da nake dukar sa. Ko da shike bai mutu ba a ranar da na duke shi, sai rana ta biyu na taras da mutuwar sa” inji shi.

Karanta wannan kuma: Obasanjo yayi gudun hijira daga kasar Najeriya