Connect with us

Uncategorized

Kungiyar Kirista (CAN) ta Kaduna sun zargi Gwamna Nasir El-Rufai da shirin Rushe wa Ikilisiya

Published

on

at

Hadaddiyar Kungiyar Addini Kirista (CAN) na Jihar Kaduna sun zargi Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar da shirin sa na rushe wata Ikilisiyar Dunamis a Jihar.

Kungiyar sun bayyana hakan ne bayan da suka Ikilisiyar Dunamis Internation Gospel Centre (DIGC) na Jihar suka karbi wata wasika daga hannun manajan hukumar KAPSUDA, Fatima Bambale.

Wasikar na dauke da lamba kamar haka; PS/14/PP/ZIII/20, 624/ VOL.I/0 ‘An umurce ni da in rubuta maku da samar da takardu dama ga kadamar da Ikilisar ku’.

“An kuma bukatar ku mayar da martani ga wannan wasika ba tare da jinkiri ba cikin tsawon kwanaki bakwai da karban wasikar”.

Sakataren Kungiyar CAN na Jihar, Mista Sunday Ibrahim, ya ce “Kirista zasu tashi tsaye ga duk wata mataki na rushe mana Iklisiyu a Jihar”.

Bayan karban wasikar, Kungiyar CAN sun wallafa na su wasikar rashin amincewa da matakin da hukumar ke shirin yi.

takaitaccen wasikar na cewa; “Mun rubuta da sanar maku a wannan wasika da rashin amincewar mu da wasikar da kuka aiko mana da ita. Muna kuma tunar da hukumar ku da cewa wannan lamarin gwamnati ce ba ta mutum daya ba”.

“A doka da kuma shirin gwamnatin na ganin cewa ya dace a kadamar da hidimar addini a Jihohin kasar, mun kuma tabbatar da cewa hukumar na da sanin hanya da ta dace da sanar da duk wata sakon ta. watau ta CAN”.

“Wannan ya zafe mu, kuma wannan a garemu alama ce da shiri na hukumar KAPSUDA don dakatar da hidimar addinin Kirista a Jihar”.

Karanta wannan: Kungiyar mu ba ta siyasa ba ce, inji Kungiyar CAN.Advertisement
close button