Connect with us

Uncategorized

NAFDAC sun kame wani mai Kemis a Kano da ya boye kwayoyi mara kyau har fiye da Miliyan daya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar NAFDAC ta Jihar Kano sun kame wani mai suna Goodluck Nwadike a Jihar Kano.

Farfesa Moji Adeyeye, Darakta Janar na hukumar ta bayyana da manema labarai da cewa sun kame Mai Kemis din ne a layin lamba na 2, kasuwar Mallam Kato, a nan Sabon Garin Kano.

“An gane Goodluck ne da ajiyar mugan kwayoyi da kuma kwayoyi mara sa kyau kamar su ‘Absorb Dano da IP” inji Moji.

“Mun kuma gane da cewa Goodluck bai yi ajiyar magungunan ba a kamar yadda dokar magunan suka bukaci a yi”

“Da muka kame shi, ya bayyana da cewa ya kan sayo magunan ne a daga kasuwar Onitsha, Anambra” inji Moji a bayanin sa da manema labarai.

Farfesa Adeyeye ya kara da cewa da aka buga lissafi, magungunan sun kai kimanin kudi Miliyan daya da rabi (N1.5m).