Uncategorized
Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna sun gano shanaye 61 da aka sace
Jami’an ‘yan sandan Jihar Kaduna a ranar Asabar da ta gabata sun gano wasu shanaye 61 da ake watakila an sace su ne a baya.
An gano shanayan ne a yayin da jami’an tsaron ke yawon bincike a shiyar Kwanar Ugara da ke a hanyar Buruku ta karamar hukumar Chikum, Jihar Kaduna.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Gwamnar Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai fada da cewa bai damu ba ko da ace bai ci zaben takaran gwamnar Jihar Kaduna ba ga zaben ranar Asabar.
Malam Ahmad Abdurrahaman, Kwamishanan ‘yan sandan Jihar a bayanin shi da manema labarai a ranar Asabar a nan Jihar Kaduna ya ce “Hukumar tsaro sun gano shanayen ne a lokacin da suke yawon bincike a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2019. An gano shanayan na yawo ba makiya ko daya da ke biye da su, muna zaton kuma da cewa shanayan watakila shanayan da aka sace ne daga masu shi”.
“Da muka gane da hakan, sai muka kwashe su zuwa Hedkwatan mu da ke a Buruku” inji shi.
“Hukumar na sanar ga dukan al’umma, watakila akwai wadanda aka sace masu tumaki da shanayan don su zo da tabbacin hakan don daukar shanayan su“
Ya kuma bada tabbaci ga jama’ar Kaduna da cewa hukumar na a shirye don yaki, da daukar matakai da ta dace don magance irin wadannan matsaloli a Jihar.
“Idan kana da shaida ta musanman na bayyana cewa shanunka ya bace, kuma yana cikin shanayan da aka gano, sai ka zo da bayyana hakan” inji Malam Ahmad.
Karantan wannan kuma: Wani mai mutumi mai shekaru 35 da haifuwa ya kashe matarshi da ake kira Bulo, wai don ta hana shi yin jima’i da ita.