Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 4 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 4 ga Watan Maris, 2019
1. Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wadanda zasu kasance cikin rukunin sa
Shugaban kasan Nejeriya da ya lashe zaben kujerar shugabancin kasa daga Jam’iyyar APC a zaben watan Fabrairu da ta gabata, Muhammadu Buhari, ya bayyana da cewa wadanda ke da adalci da kuma gurin ganin ci gaban kasar Najeriya ne kawai zai sanya a rukunin da zasu yi shugabanci da shi a wannan karo ta biyu a mulki.
Shugabana ya bayyana hakan ne a wata zaman liyafa da yayi tare da Mata da Matasan Jam’iyyar APC a ranar Asabar da ta gabata don murna da nasaran lashe zaben 2019.
2. Sambo Dasuki ya saura da rai a hannun hukumar DSS
Bayan jita-jita da ya mamaye yanar gizo da zargin cewa tsohon shugaban bada shawara ga lamarin tsaron kasa, Sambo Dasuki ya mutu, an bayyana ga mutane da cewa bai mutu ba, yana a kame ga hannun hukumar DSS.
Naija News Hausa ta gane da wannan gabatarwan ne kamar yadda wani marubuci da mai yada yawu ga labarai a kasar, Yushau Shuaib ya bayyana da cewa lallai karya ne zargin da jita-jita da ake yi. “Dasuki na da rai, kuma yana a kame wajen hukumar DSS” inji shi.
3. Zamu binciki hukumar INEC dalilin da ya sa suka daga zabe – Sanata Gaya
Sanata Kabiru Gaya da ke a karkashin Jam’iyyar APC ta Jihar Kano ya bayyana da cewa gidan Majalisa zata binciki dalilin da ya sa hukumar gudanar da zaben kasa, INEC suka daga zaben 2019 a Asabar ta farko da ya kamata a fara gudanar da zaben.
Kabiru ya gabatar da hakan ne ga manema labarai a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris da ta gabata.
4. Buhari bai da sanin matakin Oshiomhole a matsayin ciyaman na Jam’iyyar APC – inji Okorocha
Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya fada da cewa bai zaci shugaba Muhammadu Buhari na da sanin matakin da ciyaman na Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya dauka ba.
Naija News ta gane da cewa Adams Oshiomhole ya gabatar a baya da cewa ya tsige Rochas Okorocha daga Jam’iyyar APC.
5. Mahara da bindiga sun kashe mutane 6, sun kuma raunana mutane 8 a Jihar Kaduna
‘Yan hari da bindiga sun kai wata sabuwar hari a Jihar Kaduna inda suka kashe har mutane shidda (6) da barin mutane 8 da raunuka sakamakon harbin harsasai.
Naija News Hausa ta gane da cewa maharan sun kai wa kauyan Sabon Sara hari, kauyan na kusa ne da kauyan Kidandan a karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna, a ranar Asabar da ta gabata misalin karfe 1:30 na saifya.
6. Dalilin zai sa Atiku Abubakar ya fadi a kotun kara – Agbakoba
Lauyan Kara, Mista Olisa Agbakoba (SAN), ya bayyana da cewa zai zama da wuya dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ci nasara ga karar da ya kai a kotu game da zargin cewa zaben Kudun kasar ta rage yawa daga kuri’un da aka jefa.
Agbakoba a wata zaman tattauna da manema labaran Vanguard, ya fada da cewa shi a ganin shi ya kamata ne ace Atiku Abubakar na daya daga cikin manya masu fadi a ji a kasa, bawai ya shiga batun karar zabe ba.
7. Mutane 50 sun bace bayan wata fashewar wutar mabulbulan mai a Jihar Bayelsa
Kimanin mutane 50 aka bayar a rahoto da cewa sun bace bayan wata mumunar fashewar wuta a mabulbulan mai a yankin Jihar Bayelsa.
Mun gane ne a Naija News Hausa da cewa hadarin ya faru ne a yankin Nembe a Jihar Bayelsa bayan da mabulbulan mai ya fashe a ranar Jumma’a, 1 ga watan Maris da ta gabata.
8. Okorocha ya tsige Oshiomhole daga matsayin Ciyaman na Jam’iyyar APC
Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar da cewa shi ya tsige ciyaman na Jam’iyyar APC ta tarayya, Adams Oshiomhole daga matsayin shi a Jam’iyyar APC.
Naija News ta gane ne da cewa Okorocha ya fadi hakan ne don mayar da martani ga zancen da Adams Oshiomhole yayi na cewa ya dakatar da Rochas Okorocha daga Jam’iyyar APC.
9. Kotu ta gabatar da kame wata shahararar ‘yar shirin Fim na Nollywood
Kotun Koli ta Jihar Legas ta gabatar da zancen kame Monalisa Chinda, shahararar ‘yar shirin fim na Nollywood ta Najeriya da zargin cewa ta ki biyar kudin harajin ta har ga tsawon shekaru shidda 6.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kotun Koli ta Jiha Legas sun gabatar da kame Jay-Jay Okocha, tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya akan rashin biyaya ga kotun da biyar harajin shi.
10. Jam’iyyar PDP za tayi wata ganawa a yau Litinin
Jam’iyyar adawa, PDP sun gabatar da cewa zasu yi wata ganawa a yau litini, 4 ga watan Maris.
Naija News ta gane da wannan sanarwan ne daga bakin kakakin jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, inda ya bayyana da cewa jam’iyyar zasu gana misalin karfe 12 na ranar yau a birnin Abuja.
Ka samu cikkakun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa