Uncategorized
Abin Al’ajabi, Wuta ta kone Masujada amma Littafi mai Tsarki basu kone ba
Allah da ikonsa, wata abin al’ajabi a yayin da wuta ta kone wata masujada a kasar U.S
Wata ikklisiya mai suna ‘Freedom Ministries Church’ a birnin Grandview, ta yankin West Virginia, a kasar U.S ta kame da wuta. Amma abin ban mamaki, duk da konewar ikklisiyar, wuta bai taba Littafai masu Tsarki da ke cikin Ikklisiyar ba, har ma da Gijiyen Yesu (Isah Almasihu), ba wanda ya kone daga cikin hatsarin wutar.
A bayanin daya daga cikin masu yaki da kamuwar wuta da suka halarci kashe wutar Ikklisiyar, ya bayyana da cewa dole sai da wasu daga cikin ma’aikatan hukumar kashe wutar suka ja da baya a yayin da suka gane wutar yayi yawan gaske.
“Amma abin mamaki duk da yawa, da azabar wutar, ba Littafi mai Tsarki ko daya da ya kone”
Mutumin da ba a bayyana sunan shi ba a rahoto, ya gabatar be da wanan a yanar gizon nishadarwa ta facebook; Ya ce “A ganewa da kuma hikimar mutum, dole ne ka zaci cewa Littatafar zasu kame da wuta duka, amma abin a haka bane. Ko daya daga cikin Litattafai masu tsarki bata kone ba” inji she.
“Ko da shike komai ya juya, al’amura basu zama daidai ba, amma Allah bai kasance haka ba” inji mai bada bayani.
Naija News ba ta iya gane sanadiyar wannan kamun wutar ba tukuna, amma bincike na akai.
Karanta wannan kuma: Iyalin mutane shida 6 sun kone kurmus da wuta a Jihar Kano.