Connect with us

Uncategorized

Ba zamu dakatar da ma’aikata daga aiki ba – inji Gwamnan Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana da cewa ba zata dakatar da ma’aikatan Jihar ba don matsalar biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu 30,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar.
Gwamnatin ta kuma bada tabbaci da cewa ta na a shirya don samar da ayuka da kuma tabbatar da cewa ba a dakatar da kowane ma’aikaci ba don kankanin albashi.

Shugabancin Jihar ta gabatar da hakan ne daga bakin Alhaji Danjuma Salau, Kwamishanan Labarai da Sadarwa ta Jihar Neja a wata zaman tattaunawa da aka yi a babban birnin Jihar Neja, Minna.

Alhaji Salau ya kara bayyana da cewa Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello na murna da godiya mara matuka ga ma’aikatan Jihar da irin kuzari da kokari ta musanman na kawo ci gaba ga Jihar.

“Gwamnatin Jihar na bada tabbacin taimakawa ma’aikata da fasaha da zai taimaka masu wajen kara kwarancewa wajen samar da ayukan su” inji shi.

Ya kara da cewa Jihar, hade da kananan hukumomi zasu zasu kuma tabbatar da samar da ayuka ga ‘yan makarata jami’a da suka kamala karatun su da kuma masu neman aiki duka a Jihar.

“Yawancin kamfanoni da ma’aikata a Jihar na bukatar ma’aika kwarai da gaske, gwamnatin Jihar za ta tabbatar da cewa ta bude hanyoyin aiki ga wadanda ke neman aiki, musanman ‘yan makarantar Jami’a da suka kamala karatun su”.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya gabatar da cewa Jihar Neja, Jiha ce ga masu yada jari.