Uncategorized
Kannywood: Takaitaccen Tarihin Rahama Sadau
Wannan shine takaitaccen Labarin Shararriyar ‘yar shirin fim na Kannywood, Rahama Sadau
A yau 6 ga Watan Maris, shekara ta 2019, Naija News Hausa na murnan gabatar maku da taikaitaccen bayani game da rayuwar Rahama Ibrahim Sadau. Daya daga cikin shahararrun ‘yan wasan kwaikwayon Hausa da aka fi sani da Kannywood.
Labarin Haifuwa:
An haifi Rahama Ibrahim Sadau ne a ranar 7 ga watan Disamba, a shekarar 1993 kamar yadda ‘Wikipedia’ ta bayar. Ta kuma yi zaman rayuwarta ne da iyayen a Jihar Kaduna tun daga haifuwa.
Labarin Karatun Rahama Sadau:
Rahama Sadau tayi karatun jami’a na farko ne a Makarantan Fasaha ta Jihar Kaduna da aka fi sani da (Kaduna Polytechnic), inda ta karanta ‘Business Administration’ a matsayin kwas na ta.
Sadau, ta kara da karatun ta na karanta kwas din ‘Human Resource Management‘ a wata babban Makarantar Jami’ar Eastern Mediterranean University in Northern Cyprus a shashin bincike akan sana’a da tattalin arziki.
Shigar Rahama Sadau a shirin Fim:
A wata sanarwa, Rahama ta bayyana da cewa ta shiga ra’ayin shirin fim ne tun lokacin da take karamar yarinya, watau tun lokacin da ta ke makarantar Firamare har zuwa Sakandari.
“Shirin Fim ya shiga rayuwa na ne tun lokacin da ni ke karamar yarinya. Na yi shigar ajin rawa a karama, amma kullum ina da hangen nesa da ganin cewa wata rana zan zama babba fiye da hakan” inji ta.
Kannywood:
Rahama Ibrahim Sadau ta samu shigar shirin fim na Kannywood ne a shekara ta 2013, bayan da ta hadu da kwararren dan shiri, darakta da ambasada, Ali Nuhu. Haduwar Rahama da Ali Nuhu ya sa tauraron ta ya haska kwarai dagaske, musanman bayan da ta fito cikin shirin fim na farko da taken Gani Ga Wane.
Rahama Sadau ta fito daga cikin shiri kamar;
Da Kai Zan Gana, Mai Farin Jini, Sabuwar Sangaya, Sirrin Da Ke Raina, So Aljannar Duniya, Suma Mata Ne, Farin Dare,
Gani Ga Wane, Aljannar Duniya, Adam, Ba Tabbas, MTV Shuga Naija 2017, Rariya, Rumana, Sons of the Caliphate 2016, The Other Side 2016, Jinin Jiki Na, Hujja, Garbati, Kaddara Ko Fansa, Kisan Gilla, Mati da Lado, da sauran su.
Kyautannai:
Rahama, a cikin dan kanancin lokacin da ta shiga shiri da kannywood; ta sami kyautuna da daman da ya kara haska ta.
Rahama na da Kyautunai kamar; Fitacciyar ‘yar wasa a City People Awards – 2014, Bidbits – 2014, Arewa Films Awards hade da Afro Hollywood Awards a shekara ta 2015, Fitacciyar ‘yar wasan Afrika – 2015, Fuskar Kannywood – 2016, da dai sauran su.