Labaran Najeriya
Ku dauki kaddarar nasarar Muhammadu Buhari – inji Sultan na Sokoto
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 5 ga Watan Maris, 2019 ya marabci manyan sarakunan gargajiya ta kasar Najeriya a fadar sa ta birnin tarayyar kasar Najeriya, Abuja.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa manyan sarakunan sun kai ziyarar ne ga shugaba Muhammadu Buhari a jagorancin Sultan na Sokoto, babban shugaban kungiyar sarakunan Najeriya (NCTRN), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, don taya shugaba Buhari murna da lashen tseren zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da aka yi a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairun.
Sarki Muhammad Sa’ad a bayanin sa wajen ziyarar shugaba Buhari ya karfafa ‘yan Najeriya duka da daukar kaddarar nasarar shugaba Muhammadu Buhari ga zaben shugabanci na karo biyu a kasar.
“Na shawarci al’ummar Najeriya da daukar wannan nasara a matsayin kaddara da kuma gane da cewa wannan nufin Allah ce da ganin shugaba Buhari ya koma ga kujerar mulkin kasar Najeriya, kuma babu mai iya canza wannan” inji shi.
“Wannan nufin Allah ne kuma muka kira ga kowa da kowa don goyon bayan wannan nasarar wajen samar da ci gaba da zamantakewar kasa Najeriya”
Sarkin ya kuma bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ganin cewa ya gudanar da shugabancin sa a hanyar da ta dace da kuma tabbatar da cewa bai nuna banbanci ba ga kowa.
Karanta wannan kuma: Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana irin mutanen da zai sanya a shugabanci a mulkin sa ta karo biyu.