Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 6 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 6 ga Watan Maris, 2019

1. Dan takaran shugaban kasa ya yi karar Buhari da Atiku ga kotu

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar National Rescue Movement (NRM), Alhaji Usman Ibrahim ya yi karar shugaba Muhammadu Buhari da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a kotu.

Advertisement
Advertisement

Naija News ta gane da cewa Ibrahim-Alhaji yayi karar ne da zargin cewa ‘yan takara biyun sun kashe kudi fiye da yadda dokar kasa ta bayar akan hidimar siyasa.

Advertisement

2. IGP na ‘yan Sanda ya bada umarni dakatar da amfani da lambar mota da ake rufewa

Shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar Najeriya, Insfekta Janar Ag. IGP Mohammed Adamu, ya bukaci dakatar da amfani da lambobin mota da babura da ake rufewa ga wadanda doka bata bayar da dama ba a garesu a kasar.

Advertisement
Advertisement

Naija News Hausa ta samun tabbacin hakan ne a yayin da shugaban ya gabatar da hakan a ranar Talata 5 ga watan Maris, 2019 da ta gabata. IGP yayi hakan ne don magance wasu matsaloli da ke tasowa lokacin zabe.

Advertisement

3. Hukumar EFCC sun saki Turaki, Darakta Janar na hidimar zaben Atiku

Hukumar kula da hidimar tattalin arzikin kasa da kare cin hanci da rashawa (EFCC) sun saki Tanimu Turaki, mataimakin darakta janar ga hidimar zabe na dan takaran shugaban na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Advertisement

Naija News ta gane da hakan ne a ranar Talata da ta gabata da cewa hukumar ta saki Tanimmu.

Advertisement
Advertisement

4. Jam’iyyar APC na kokarin tsananta karar da Atiku ke yi ga Buhari – inji CUPP

Kungiyar jam’iyoyin kasa (CUPP) na zargin jam’iyyar APC da tsananta da kuma kokarin dakile karar da dann takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ke yi game da rahoton zaben shugaban kasa da kuma nasarar Muhammadu Buhari ga zaben 2019.

Advertisement

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Atiku Abubakar ya bayyana rashin amincewar sa game da sakamakon zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

Advertisement

5. Shugaba Buhari yayi zaman tattaunawa da hukumomin tsaro game da zaben Gwamnoni

A ranar Talata da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawa ta musanman da hukumomin tsaron kasa a birnin Abuja akan hidimar zaben gwamnonin Jiha da za a yi a ranar Asabar ta gaba.

Advertisement
Advertisement

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa hukumar INEC ta gabatar da cewa ranar Asabar, 9 ga watan Maris a matsayin ranar zaben Gwamnonin Jiha ta kasar Najeriya.

Advertisement

6. An saki Sanata Dino Melaye daka kotun kara

A ranar Talata da ta wuce, Kotun kara ta saki sanatan Najeriya daga Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye.

Advertisement

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa an gabatar da kame Sanata Melaye da zargin kisan kai hade da wasu zargi na lallace kayan jami’an ‘yan sandan kasar.

Advertisement
Advertisement

7. Tinubu yayi karyace zaben hana Gwamna Ajimobi da hidimar neman zabe a Jihar Oyo

Babban shugaban Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da jita-jitan cewa ya dakatar da Gwamna Abiola Ajimobi, gwamnan Jihar Oyo daga kadamar da hidimar neman zaben sa.

Advertisement

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa hukumar INEC ta gabatar da cewa ranar Asabar, 9 ga watan Maris a matsayin ranar zaben Gwamnonin Jiha ta kasar Najeriya.

Advertisement

8. Hukumar EFCC ta saki surukin Atiku

Hukumar EFCC sun saki Babalele Abdullahi, surukin dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da suka kame a baya.

Advertisement
Advertisement

An gabatar da hakan ne a shafin yanar gizon nishadarwa ta twitter, kamar yadda Segun Sowunmi, kakakin yada yawun Atiku Abubakar ya sanar.

Advertisement
Advertisement

Ka samu cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement