Connect with us

Labaran Najeriya

Mutumin Bauchi, Haruna da ya yi wankar kwata don murna ga nasarar Buhari, ya Mutu

Published

on

Wani matashin Jihar Bauchi, mai suna Bala Haruna, da muka ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa yayi wanka da ruwar chabbi don nuna irin nasa murna ga nasar shugaba Muhammadu Buhari, ya mutu.

Mun gane a Naija News da cewa Haruna yayi alkawarin cewa da zarar an gabatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara da kuma wanda ya lashe tseren takaran shugaban kasa na shekarar 2019, zai shiga cikin kwata ya kuma sha ruwar kwata don murna.

Da hakan ne Bala Haruna ya cika alkawalin sa bayan da hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben ranar Asabar 23 ga wata Fabrairu da aka yi a kasar.

Haruna ya kuma rabar da hoton kansa a cikin kwata a yanar gizo don bayyana ga jama’a da cika alkawalin sa.

Mun samu rahoto a Naija News da safen nan da cewa Haruna ya mutu ranar Talata, 5 ga watan Maris. ‘Yan kwanaki kadan dan shan ruwar kwata don murnan nasarar Buhari.

A bayannin manema labaran Guardian, “An rutsa Haruna ne zuwa asibiti bayan da yayi ta kukar ciwon ciki da kuma zubar jini sakamakon ruwar kwata da ya sha”

Naija News Hausa ta gane d cewa yawancin mutane daga arewacin kasar sun gabatar da murnan su ga nasarar shugaban a hanyoyi da dama. kamar yadda muka sanar da cewa wata yarinya ta fashe da kuka da hawaye a yayin da take gabatar da kanta cikin wata bidiyo da murna akan nasarar Buhari ga zaben 2019.