Connect with us

Labaran Najeriya

Ban mutu ba, Ina Lafiya Kalau – Masoyin Buhari da ya sha ruwar kwata

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa wani masoyin Shugaba Muhammadu Buhari yayi wankar kwata don murna akan nasarar Buhari ga lashe zaben kujerar shugabancin kasar Najeriya.

Jita-jita mutuwar Aliyu ya mamaye ko ta ina a layin yanar gizo duka, amma abin mamaki Aliyu Mohammed Sani ya fito da bayyana da cewa bai mutu ba. kamar yadda gidan jaridan Daily Trust ke bada tabbacin haka.

“Alkawari ne nayi da cewa idan har shugaba Muhammadu Buhari ya lashe tseren takaran kujerar shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu ga zaben 2019, zan yi wanka da ruwar kwata, zan kuma sha kwata”

“Na kuma cika alkawari na. A yayin da aka gabatar da Buhari a matsayin mai nasara ga zaben, na shiga kwata kamar yadda na yi alkawali, na kuma sha ruwar kwatan a gaban jama’a. Duk wata zancen cewa na mutu sakamakon aman jini ko wata ciwon ciki, ba gaskiya bane. Ina lafiya lau, kuma ina garau” Inji Aliyu.

Naija News Hausa ta iya gane da cewa Aliyu na da aikin hannun sa na fenti.

“A yadda ni ke gabatar da wannan bayanin, ina shirye kan komawa Bauchi daga wata aikin fenti da ya kawo ni inda nake yanzun nan” inji shi.

Karanta wannan kuma: Karanta takaitaccen labarin Rahama Sadau, shahararrar ‘yar shirin fim na kannywood