Connect with us

Uncategorized

Bidiyo: Kalli bayanin Atiku game da zaben gwamnoni da za a yi ranar Asabar

Published

on

Dan takaran shugaban kasar na Jam’iyyar PDP ga tseren zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar yayi wata sabuwar bayani game da zaben gwamnoni da ta gidan majalisar jihohi da za a yi ranar 9 ga watan Maris, 2019 kamar yadda hukumar INEC ta sanar a baya.

Atiku yayi kira ga al’ummar Najeriya duka da fitowa ranar Asabar don jefa kuri’ar su ga dan takaran su ga zaben gwamnoni.

Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar da wannan sanarwan ne ga ‘yan Najeriya a ranar Alhamis a yanar gizo cikin wata bidiyo da aka tsarafa. Ya bukaci ‘yan Najeriya da fita ranar Asabar don jefa kuri’ar su a matsayin ‘yan kasa.

Ya kara da shawartan ‘yan jam’iyyar PDP duka da cewa kada su raunana da yadda zaben shugaban kasa ya kasance. Ya ce “ku fito da yawar ku ranar Asabar don zaban dan takaran jam’iyyar PDP ga zaben gwamnoni da kuma ta gidan majalisar jiha” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Atiku Abubakar yace bai amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, 2019 ba.

“Ka da ku raunana da yadda zaben shugaban kasa ya kasance. Mun kan bincike da daukar mataki akan doka ga yadda aka tafiyar da zaben” inji Atiku

Kalli bidiyon a kasa;