Connect with us

Uncategorized

Jam’iyyar PDP ta Jihar Neja sun gabatar da Azumi don nema sa’a ga Umar Nasko, dan takaran Gwamnan Jihar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Zaben gwamnonin Jihar kasa ta bana ya bayyana da zafi da gaske a yayin da Jam’iyyar PDP suka gabatar da azumin kwana biyu da mambobin ta don nema sa’a da nasara ga dan takaran su na kujerar gwamnan Jihar Neja.

Naija News Hausa ta gane da cewa Alhaji Umar Mohammmed Nasko, dan takaran kujerar gwamnan Jihar Neja daga jam’iyyar adawa ta PDP ne babban dan takara da ke jayayya da Alhaji Abubakar Sani Bello (LOLO), gwamna da ken kan mulkin Jihar a halin yanzu.

Jam’iyyar sun gabatar da hidimar azumi na kwana biyu ne don neman fuskar Allah ta wajen addu’a don samun nasara ga Jam’iyyar ga zaben tseren kujerar Gwamnan Jihar a shekara ta 2019.

Hidimar azumin zai dauki tsawon kwana biyu ne kawai, watau daga ranar Alhamis 7 ga watan Maris zuwa ranar Jumma’a 8 ga Watan Maris, 2019. Kamar yadda jam’iyyar suka gabatar.

Ga sanarwan kamar haka;

AZUMI! AZUMI!! AZUMI!!!

Sanarwa ga duk masoyan Umar Nasko, Ana bukatar mu duka da azumin kwanaki biyu, daga ranar Alhamis zuwa Jumma’a don neman fuskar Allah ga nasarar zaben gwamna.

Naija News Hausa ta kuma gane da cewa, Alhaji Tanko Beji, ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar ya bukaci masoya, al’ummar duka da ke goyon bayan jam’iyyar PDP da su fito da yawar su ranar Asabar ta makonnan don jefa kuri’ar su ga dan takaran su.