Connect with us

Uncategorized

Ku guje wa halin tashin hankali ga zabe, Sarkin Kani ya gayawa ‘yan takaran Gwamnoni Jihar

 

Kimanin ‘yan takaran kujerar gwamna 31 a Jihar Kano sun sanya hannu ga takardan zamantakewar lafiya a Jihar Kano.

Sanya hannu ga takardan ya halarci ‘yan takara kamar su; Abdullahi Ganduje, daga jam’iyyar APC, Alhaji Abba Yusuf dan takaran kujerar gwamna daga jam’iyyar PDP da Salihu Sagir Takai, dan takaran gwamna daga jam’iyyar (PRP) da sauran su.‎

Muhammadu Mahraz, a wakilcin sarkin Kano ya shawarci ‘yan takara duka da cewa su guje wa halayan da zai tayar da hankali mutane a lokacin zabe da kuma bayan zabe.

“Ina shawartan ku da janye wa duk wata shiri da zai kai ga hallaka dukiya ko kisan kai a lokacin zaben ranar Asabar da kuma bayan zaben” inji Mahraz.

“Muna bukatar zaman lafiya kamin zabe, lokacin zabe da kuma bayan zabe a kasar” inji shi.

An gudanar da hidimar sanya hannun ne a jagorancin shugaban kungiyar zamantakewar lafiya ta Jihar Kano, Farfesa Ibrahim Umar, da kuma babban Bishaf na Ikklisiyoyin Jihar Kano, Rt. Rev. John Niyiring da kuma mamba na kungiyar zamantakewar lafiyar kasa na tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari.‎

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa ‘yan takaran shugaban kasa sun sanya hannu ga takardan zamantakewar lafiyar kasa kamin zaben shugaban kasa ta 2019.

“Wannan hidimar sanya hannu ga takardan zamantakewar lafiya na da muhimanci kwarai musanman don taimakawa wajen gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali” inji bayanin kwamishanan ‘yan sandan Jihar Kano, Muhammad Wakili.

“Muna kokarin hada kai da sauran hukumomin tsaron kasa don gudanar da hidimar tsaro ta kwarai wajen zabe da kuma bayan zaben”

Ya kuma shawarci ‘yan takara duka da cewa su guje wa furcin da zai iya tayar da tanzoma da kuma matsala wajen zaben ranar Asabar.

Karanta wannan kuma: Ku dauki kaddarar nasarar Muhammadu Buhari – inji Sultan na Sokoto

Advertisement
close button