Uncategorized
Zaben Gwamnoni: Ku sake zaben miji na ga komawa kujerar Gwamna – Ummi El-Rufai

Hajiya Ummi El-Rufai, matan gwamnan Jihar Kaduna, a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, 2019 da ta gabata, ta roki matan jihar da su goyi bayan gwamna Nasir El-Rufai, mijinta da ganin cewa ya lashe zaben gwmanonin Jihar ga zaben ranar Asabar ta makonnan.
Ummi ta gabatar da wannan ne a yayin da ta ke bayani da manema labaran NAN a wata hidimar zagayen GIDA da GIDA da jam’iyyar APC suka gudanar a Jihar.
“Mun zo ne don gabatar da murnan mu da godiya ga al’umma don irin goyon baya da kuka nuna wajen fitowa da yawar gaske don jefa wa shugaba Muhammadu Buhari kuri’un ku ga zaben shugaban kasa da aka yi a baya ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019″
“Muna kuma kira ga jama’a duka don kara fitowa don nuna goyon baya da kuma jefa wa dan takaran kujerar gwamna, Nasir El-Rufai kuri’ar ku ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2019. ” inji Hajiya Ummi.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Nasir El-Rufai ya ce, “Ko da ya sanya Fafa Roma a matsayin abokin takaran shi, Kiristocin Jihar Kaduna ba za su zabe shi ba”.
Hajiya Ummi ta kara godiya ga mata, musanman yadda suka fito wajen zaben shugaban kasa. Ta kuma bukace su da kara fitowa don zaban mijinta ga shugabancin Jihar a karo ta biyu.
Ta kuma shawarci al’ummar jihar da cewa su kwantar da hankalin su daga tsoron wata matsala. su kuma guje wa duk wata halin tashin hankali a wannan lokaci har ma ga bayan zabe.
Karanta wannan kuma: Abin Al’ajabi, Wuta ta kone Masujada amma Littafi mai Tsarki basu kone ba