Connect with us

Uncategorized

Babu tashin hankali ko kadan a Zaben Gwamnoni a Neja – inji Dauda Shehu

 

A yayin da ake cikin hidimar zaben gwamnoni da majalisar wakilai ta jiha, a yau Asabar 9 ga watan Maris 2019, mun samu tabbaci daga Jihar Neja da cewa zaben na tafiya daidai yadda ya kamata ba tare da wata tashin hankali ba.

Naija News Hausa na da sanin cewa lashe kujerar mulkin Jihar Neja a halin yanzu na tsakanin jam’iyyu biyu, watau APC da PDP.

Mun samu tabbaci a Naija News daga bakin Dauda Alhaji Shehu, Mai yada labarai da shawarwari ga Ciyaman na karamar Mariga. Ya bayyana da cewa hidimar zabe a Jihar na tafiya yadda ya kamata ba tare da tashin hankali ba.

“Mutane sun fito da jefa kuri’un su. Ba wata tashin hankali a halin yanzu, hidimar na kuma tafiya yadda ya kamata” inji shi a yadda ya gabatar ga Naija News.

Mun ruwaito a baya da cewa jam’iyyar PDP a Jihar Neja sun gabatar da arzumin kwana biyu ga dan takaran kujerar gwamna na Jihar daga jam’iyyar PDP, Alhaji Umar Nasko. Jam’iyyar ta gabatar da azumin kwana biyun ne don neman fuskar Allah ga lashe zaben kujerar Gwamna ga Umar.

Ko da shike mun iya gane da cewa Alhaji Abubakar Sani Bello (LOLO), Gwamnan Jihar da ke akan mulki yanzun na tafiyar da wasu ayuka a wasu yankunan Jihar da watakila zai iya sa ya lashe zaben.

Mun kuma tuna a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan Jihar Neja sun yi wata zaman ganawa don tattaunawa a Minna, babban birnin Jihar, game da zancen yadda manyan hanyoyin jihar suka lallace duka. Mun kuma iya ganewa a Naija News Hausa da cewa a baya an dakatar da manyan motoci da bin wasu hanyoyi a Jihar saboda hadari da kuma yadda hanyar tayi mumunar lallacewa. musanman hanyar da ta bi daga Ilori ta ratsa Jihar Neja zuwa hanyar Jihar Sokoto.

A karshen zaben yau, kuri’un al’ummar Jihar zai iya bayyana ko wanene suke so a Jihar a matsayin Gwamna.

Karanta wannan kuma: Ban damu ba, ko da na fadi ga zabe, tun da Buhari ya kashe kujerar mulki – inji El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna.

Advertisement
close button