Connect with us

Uncategorized

APC: Abdulrazaq ya lashe kujerar gwamnan Jihar Kwara – INEC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran kujerar Gwamna daga jam’iyyar APC, Mista Abdulrahman Abdulrazaq, ya lashe tseren takaran gwamnan Jihar Kwara ga zaben ranar Asabar.

Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), ne suka gabatar da wannan bayan da suka gama kidayan kuri’ar ‘yan takaran kujerar gwamnan Jihar. Abdulrazaq ya lashe tseren takaran da kuri’u 331,546 fiye da dan adawan shi daga jam’iyyar dimokradiyya (PDP) Mista Abdulrazaq Atunwa, da ya samu kuri’u 114,754.

Naija News Hausa ta iya gane da cewa Abdulrahman Abdulrazaq ya lashe dukan zaben kananan hukumomin jihar da kuri’u fiye da dan adawan sa.