Connect with us

Uncategorized

APC: Sambawa ya lashe kujerar Gidan Majalisar Jihar Kebbi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), ta gabatar da dan takaran kujerar gidan majalisar jiha daga jam’iyyar APC, Alhaji Umoru Sambawa, a matsayin mai nasara ga zaben gidan majalisar karamar hukumar Maiyama ta Jihar kebbi.

An gabatar da hakan ne bayan da aka yi kidayar kuri’un zaben da aka yi ranar Asabar 9 ga watan Maris da ya gabata. Babban Malamin zaben jihar, Dakta Zuni Aminu da ke a babban makarantar jami’ar Fasaha ta birnin Kebbi (FUBK), ya bayyana a rahoton sa na kuri’un da aka jefa a Jihar da cewa Sambawa ya lashe zaben ne a yayin da ya samu kuri’u dubu 40,180 bisa dan takaran kujerar majalisar daga jam’iyyar PDP, Alhaji Balarabe Hassan da ya samu kuri’u 1,420.

Dakta Aminu ya kara da gabatar da sauran ‘yan takara da suka fita tseren, watau kamar; Aminu said Alhaji Abdulwasiw Yunusa daga jam’iyyar (SDP) da ke da kuri’u 23, shi kuma dan takara daga jam’iyyar JNPP, Alhaji Tonko Jamilu ya samu kuri’u hudu (04).

Hukumar haddadiyar ‘yan jaridan Najeriya (NAN) sun gabatar da cewa jam’iyyar APC ne ta lashe dukan yankuna goma sha daya (11) da ke a karamar hukumar Maiyama ta Jihar Kebbi.

Ka bi wannan layin Hausa.NaijaNews.Com a nan ne zamu sanar da sauran rahotannin Jihohi ga zaben ranar Asabar da ta gabata.