Connect with us

Uncategorized

Dan Kunar Bakin Wake ya tayar da Bam kusa da wata Ikklisiya a Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Lahadi, 10 ga watan Maris 2019, wani dan kunar bakin wake ya hari yankin Shuwa da ke a karamar hukumar Madagali ta Jihar Adamawa da Bam.

Rahoto ta bayar da cewa mumunar harin ya faru ne a missalin karfe bakwai da rabi (7:30am) na safiyar Lahadi a nan daidai da wata Ikklisiya da Kirista ke sujadar su.

Wani mazaunin anguwar ya bayyana da cewa a ganewar su, dan kunar bakin waken na da niyyar ne daman ya hari masujadan, amma bai kai ga isa wajen ba da Bam din ya tashi da shi.

Naija News ta gane da cewa kauyan Shuwa bai da nisa sosai da Madagali, Kilomita 30km ne kawai ke a tsakanin su.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a yau da cewa hukumomin tsaron kasa sun kashe ‘yan ta’adda 50 da kuma kame daya da rai.

An kara gabatar da cewa dan kunar bakin waken ya mutu ne hade da mutum guda da ke a wajen lokacin da Bam din ya fashe da shi kamin isa ga Ikklisiyar da ya ke kokarin kai hari, kamar yadda aka bayar a rahoto.

Ko da shike ba cikakken bayani game da hakan tukunna a lokacin da muka samu wannan rahoto, amma duk wata karin bayani zai biyo baya a wannan shafi, idan har mun samu hakan.