Connect with us

Uncategorized

Kalli Yadda Wamako ya lashe runfar zaben sa da kuri’u

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A zaben ranar Asabar da aka yi na gwamnoni da gidan majalisar wakilan jiha, Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, ya lashe runfar zaben sa da kuri’u.

Naija News Hausa ta gane da cewa Wamako na goyon bayan dan takaran kujerar gwamnan jihar ne daga jam’iyyar APC. Ya Wamako ya kuma yi kokarin lashe ma dan takaran kuri’un runfar zaben sa mai lamba 007/003 da ke a Gidan Jadji.

Mun kuma gane da cewa dan takaran kujerar gwamna na Jihar daga jam’iyyar APC, Aliyu Ahmed ya samu kuri’u 442 ne a runfar zaben, shi kuma dan takaran jam’iyyar PDP, Aminu Tambuwal ya samu kuri’u 98 a runfar zaben. Aminu Tambuwal ne ke kan kujerar mulkin gwamnan Jihar Sokoto a halin yanzun kamar yadda muke da sani a Naija News.