Connect with us

Uncategorized

Ba mu amince da sakamakon kuri’ar zaben Gwamnan Jihar Kaduna ba – inji PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa hukumar gudanar da zaben kasa sun gabatar da Gwamna Nasir El-Rufai a matsayin mai nasara ga lashe tseren takaran zaben kujerar Gwamnan Jihar Kaduna ga zaben ranar Asabar da aka yi a Jihar.

A yau Litinin, 11 ga Watan Maris, shekara ta 2019, Jam’iyyar PDP, bayan da hukumar INEC ta gabatar da sakamakon zaben, sun bayyana da cewa basu amince da rahoton zaben ba.

“Ba mu amince da sakamakon da hukumar gudanar da zaben kasa, INEC suka gabatar da ita ba. Sakamakon bai bayyana gaskiyar kuri’un da mutane suka jefa ba a Jihar” inji PDP.

Wakilin Jam’iyyar PDP na Jihar, Mista Jerry Ishaya, a yayin da ya ke gabatarwa a gidan kirgan zaben Jihar, ya ce Jam’iyyar mu ba ta amince da wannan ba sakamakon ba.

Ishaya bayyana da cewa wakilan jam;’iyyar PDP ta Jihar sun gabatar ga shugabannan jam’iyyar da cewa hukumar bata yi amfani da Na’urar diban katin zabe ba a yawancin runfunan zaben jihar.

“Mun wallafa wasikai ga hukumar INEC game da wannan, da cea ba a yi amfani da na’urar diba katin zabe ba a yankunan Jihar”. Wakilan mu kuma sun bayyana mana da cewa jami’an tsaro sun tsananta masu a wasu yankunan jihar.

“Jami’an tsaron sun hada kai da malaman zabe don aiwatar da magudi da munafunci ga zaben” inji Ishaya.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Hari da bindiga sun sace Surukin Gwamnan Jihar Katsina, Gwamna Aminu Masari