Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli hotunan ziyarar abokannan Shugaba Buhari tun shekarar 1953 a Daura

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta gano hotunan ziyarar abokannan shugaba Muhammadu Buhari da suka yi makaranta tare tun daga yarantaka a ziyarar da suka kai wa shugaban a lokacin zaben gwamnoni a garin Daura.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari sun shiga garin Daura kwana biyu kamin zaben Gwamnoni da ta Gidan Majalisar Jihohi kamar yadda hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) suka gabatar.

Mun kuma iya gane da cewa tsohin sun yi karatun makaranta ne tare da shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da suke yara.

Abokannan sun ziyarci Buhari ne don taya shi murna ga nasarar lashe kujerar mulkin kasar Najeriya a karo ta biyu.

Ga hotunan a kasa kamar yadda muka samu a shafin nishadarwa ta facebook;