Connect with us

Uncategorized

Aikin mu na kare yancin Al’umma ne – Yan Sandan Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya ta Jihar Kano, sun gabatar da dalilin da ya sa ba su harbe mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishanan Kananan Hukumomin Jihar, Alhaji Murtala Sule Garo a dakin kirgab zaben Jihar da ke karamar hukumar Nassarawa, a ranar Lahadi da ta gabata.

A wata sanarwa a shafin Naija News ta turanci, mun sanar da cewa Gawuna da Garo na cikin dakin kirgan zaben da ke a karamar hukumar Nasarawa a ranar Lahadi da ta gabata lokacin da farmaki ya tashi a dakin kirgan. Har an bayyana da cewa wasu matasa da ke biye da kwamishanan sun yage takardan sakamakon zaben da hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ke amfani da ita.

DSP Haruna Abdullahi, Mai yada labarai ga jami’an tsaron yankin, ya fada a bayanin shi da manema labarai da cewa “An koya mana ne yadda zamu kare rayukar al’umma da kuma tattalin arzikin ‘yan kasar Najeriya. Aikin mu kuma ta bada daman kame duk wanda ya karya doka da kuma shar’anta shi ko ita akan doka. Ba a koya mana kissa ba” in ji shi.

“Aikin mu na jami’an tsaron jihar Kano itace ganin cewa mutane sun yi biyayya ga doka, amma ba wai kashe mutane ba. mun kuma kame wadanda suka karya doka a dakin kirgan zaben”

Abdullahi ya kara da cewa hukumar su ta kame Garo da Alhaji Lamin Sani, ciyaman na karamar hukumar Nassarawa ta Jihar Kano ne da zargin barnan takardan sakamakon zabe.

“Ba mu kuma kame Gawuna ba kamar yadda ake zato, mun kubutar da shi ne kawai daga mawuyacin lamarin da ya faru a wajen” inji shi.

“Mun kuma kan bincike akan lamarin, zamu kuma hukumta duk wanda muka gane da karya doka” inji DSP Abdullahi.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Jam’iyyar PDP sun ki amince da sakamakon zaben kujerar Gwamnan Jihar Kaduna.