Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 12 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 12 ga Watan Maris, 2019

1. Hukumar INEC sun gabatar da cewa zaben Kano bai kai ga aminta ba

Hukumar Gudanar da Zaben kasa (INEC), da ke jagorancin zaben takaran gwamna da gidan majalisar wakilai ta Jihar Kano sun gabatar da cewa zaben kujerar gwamna bai kai ga aminta ba, akan wasu dalilai.

Naija  News Hausa ta gane da cewa hukumar, bayan da ta gabatar da kuri’un kananan hukumomin Jihar da kuma adadin sakamakon jam’iyun duka, sun gabatar da dakatar da zancen mai nasara ga zaben da cewa ba su kai ga aminta da sakamakon ba.

2. An kashe mutane 16 a Jihar Kaduna a wata sabuwar hari

Hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna a ranar Litini da ta gabata sun gabatar da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun kashe mutane goma sha shidda (16) a kauyan Barde da ke yankin Maro, karamar hukumar Kajuru. Wannan lamarin ya faru ne washe garin ranar Lahadi bayan da aka kamala zaben Gwamnoni da Gidan Majalisar Wakilai a Jihar.

Ofisan yada labaran Jami’an tsaron Jihar, DSP Yakubu Sabo, ya gabatar da hakan ne ga hadaddiyar kungiyar manema labaran Najeriya (NAN) a garin Kaduna.

3. Hukumar INEC ta cire sunan Okorocha daga sunayan Sanatoci

Sunan Gwamna Rochas Okorocha, Gwamnan Jihar Imo bai cikin sunayan sanatoci da hukumar INEC suka gabatar

Naija News Hausa na da sanin cewa akwai shirin bayar da takardan komawa ga kujerar mamban gidan majalisar dokoki da za a yi a ranar Alhamis ta gaba a Abuja, babban birnin tarayya.

4. Hukumar INEC zata bayar da takardan komawa mulki ga ‘yan Majalisai a ranar Alhamis ta gaba

Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), bayan zaben Gidan Majalisar Dokoki da ta Majalisar Wakilai, sun gabatar da cewa zasu mika takardan komawa ga kujerar shugabancin ga ‘yan majalisar duka a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris 2019 ta gaba.

Hukumar sun gabatar ne da hakan a layin nishadarwa ta twitter a ranar Litinin da ta gabata da cewa zasu yi hidimar bayar da takardan koma shugabanci ga ‘yan majalisai a birnin Abuja.

5. Jam’iyyar PDP na zargin Shugaban Hukumar INEC da goyawa APC baya

Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), sun zargi shugaban hukumar gudanar da hidimar zaben kasar Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu da bada hadin kai ga jam’iyyar APC, musanman wajen gudanar da zaben 2019.

PDP sun bayyana hakan ne akan matsalar dakatar da gabatar da nasara ga jam’iyyar PDP a jihohin da suka lashe zabe. Da kuma kin gabatar da sakamakon zaben wasu Jihohin kasar inda PDP ke nasara.

6. Gwamnatin Tarayya na zancen karar Sanata Melaye

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da zargin Sanatan da ke wakilcin Jihar Kogi ta Yamma, a gaban kotun koli da ke Maitama, Abuja, babban birnin Najeriya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, a umurnin Gwamnatin Tarayya sun zagaye gidan Sanata Melaye har tsawon mako daya don kame shi.

7. Hukumar INEC ta gabatar da nasarar zaben Kujerar Gwamnan Jihar Kano ga APC

Hukumar gudanar da hidimar zaben kasar Najeriya (INEC), ta gabatar da dan takaran kujerar gwamnan Jihar Borno daga Jam’iyyar APC, Farfesa Babagana Umara Zulum a matsayin mai nasara ga lashen tseren takaran kujerar Gwamna a Jihar Borno.

Dan takaran ya lashe zaben ne da kuri’u 1,175,440 fiye da babban dan adawan shi, Alhaji Mohammed Imam daga jam’iyyar PDP hade da sauran ‘yan takara 31 da suka fita tseren.

8. Aikin mu na kare yancin Al’umma ne – Yan Sandan Jihar Kano

ami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya ta Jihar Kano, sun gabatar da dalilin da ya sa ba su harbe mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishanan Kananan Hukumomin Jihar, Alhaji Murtala Sule Garo a dakin kirgab zaben Jihar da ke karamar hukumar Nassarawa, a ranar Lahadi da ta gabata.

A wata sanarwa a shafin Naija News ta turanci, mun sanar da cewa Gawuna da Garo na cikin dakin kirgan zaben da ke a karamar hukumar Nasarawa a ranar Lahadi da ta gabata lokacin da farmaki ya tashi a dakin kirgan

9. An gabatar da Lauyan da zai tsayawa shugaba Buhari ga karar zaben 2019

An gabatar da tsohon shugaban kungiyar alkalan kasar Najeriya (NBA), Mista Wole Olanipekun (SAN), a matsayin lauyan da zai tsayawa shugaba Muhammadu Buhari ga karar zaben 2019 da za a yi.

An gabatar ne da hakan don zargi da karar da Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa da kuma dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 ke yi ga shugaba Muhammadu Buhari akan sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019.

Ka samu cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa