Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 13 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 13 ga Watan Maris, 2019

 

1. Za a karshe sauran zabannin Jihohi a ranar 23 ga Watan Maris 2019 – inji Hukumar INEC

Hukumar kadamar da zaben kasar Najeriya (INEC, a yau Talata sun gabatar da cewa za a karshe sauran zabannin jihohi da aka daga a baya a ranar 23 ga watan Maris ta gaba.

Hukumar ta gabatar ne da hakan a wata sanarwa da Mista Festus Okoye, Ministan Yada labarai da samar da fasahar zabe ya rattaba hannu.

2. Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnonin APC a cikin Aso Rock

A ranar Talata, 12 ga watan Maris, Shugaba Muhammadu Buhari yayi zamar tattaunawa da gwamnonin da ke karkashin jam’iyar APC a nan cikin fadan shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.

Zaman tattaunawar ya halarci gwmana Yahaya Bello (Kogi); Nasir el-Rufai (Kaduna); Atiku Bagudu (Kebbi); Abdulaziz Yari (Zamfara); Abubakar Badaru, (Jigawa State); Kassim Shetima (Borno); da Kayode Fayemi ( Ekiti).

3. Shugaba Buhari ya rattaba hanu ga kwamitin sanya shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu ga amince da dokar kwamitin kadamar da jagorantan shugaban kasa ta 2019.

Naija News ta gane da cewa Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2019 a matsayin ranar gabatar da kwamitin a anan ofishin babban Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

4. Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 55, sun kuma kubutar da rayuka 760 a Jihar Zamfara

A ranar jiya Talata, 12 ga Watan Maris 2019, Rundunar Sojojin Operation Sharan Daji sun gabatar da kashe ‘yan ta’adda kamanin mutum 55 da kuma kubutar da mutane 760 da ‘yan ta’addan suka sace a baya daga kauyukan da ke Jihar Zamfara.

Jami’an tsaron sun gabatar da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar da aka kuma rattaba hannu daga wajen Babban Ofisan Yada sanarwa ga rundunar, Maj. Clement Abiade a garin Gusau, ranar Talata da ta gabata.

5. Zaben Jihar Kano ta ranar 23 ga watan Maris zai zan da mamaki ga PDP – inji Ganduje

Dan takaran kujerar Gwamna daga Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya gabatar da cewa karshen zaben kujerar gwamnan jihar Kano da hukumar INEC ta daga zuwa ranar 23 ga watan Maris zai zama da mamaki ga jam’iyyar PDP.

Mun gane a Naija News Hausa da cewa hukumar INEC ta Jihar Kano ta dakatar da sakamakon zaben gwamnan Jihar akan wata matsala da hukumar ta gane da ita.

6. Jami’an tsaro sun kame wanda ya kashe Olatoye Sugar

A kwanakin baya, ranar 9 ga watan Maris, wasu ‘yan hari da bindiga sun kashe Hon. Temitope Olatoye, dan gidan majalisar jiha da ke wakilcin Akinyele/Lagelu, da aka fi sani da suna ‘Sugar’.

Kwamishanan ‘yan sanda ta Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu da mataimakin Insfekta Janar na jami’an tsaron Jihar, Mista Leye Oyebade, a ranar Litinin da ta gabata, sun bayyana da cewa mutum guda ne suka iya gane da kisan Mista Olatoye.

7. Dalilin da ya sa na yi watsi da Mikel Obi da Iheanacho – Gernot Rohr, kocin kwallon kafan Najeriya

Babban Kocin ‘yan wasan kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya,  Gernot Rohr, ya gabatar da cewa ya yi watsi ne da dan wasan kwallon kafan Najeriya, Kelechi Iheanacho da John Obi Mikel ga wasan su a kasar Seychelles da kasar Masar, saboda rashin nuna kiyayya da kuma kuzarin ‘yan kwallon.

Naija News na da sanin cewa ana shirya ‘yan kwallon ne gaban wasan kwallon kafan Afrika ta tarayya da ke gaba.

8. ‘Yan Hari da bindiga a yau sun kashe dan shekara 6, da kuma sace mutane ukku a Katsina

A yau Talata, da safiyar nan, ‘yan hari da bindiga a Jihar Katsina sun kashe dan shekara 6 da kuma sace mutum ukku a wata sabuwar hari a garin Kankara.

Rahoto ta bayar da cewa mumunar harin ya faru ne da safiyar yau, a yayin da ‘yan hari da bindigan suka hari daidai gidan Malam Adamu da ke a Kofar Yamma, a nan anguwar Matsiga, inda ‘yan harin suka kashe yaron mai shekara 6, suka sace mutum ukku da kuma barin wani yaro mai shekaru 8 da raunin bindiga.

Ka samu cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa.