Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 55, sun kuma kubutar da rayuka 760 a Jihar Zamfara

Published

on

at

A ranar jiya Talata, 12 ga Watan Maris 2019, Rundunar Sojojin Operation Sharan Daji sun gabatar da kashe ‘yan ta’adda kamanin mutum 55 da kuma kubutar da mutane 760 da ‘yan ta’addan suka sace a baya daga kauyukan da ke Jihar Zamfara.

Jami’an tsaron sun gabatar da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar da aka kuma rattaba hannu daga wajen Babban Ofisan Yada sanarwa ga rundunar, Maj. Clement Abiade a garin Gusau, ranar Talata da ta gabata.

Ya bayyana da cewa rundunar sun ribato mugayan makamai daga ‘yan ta’addan da kuma shanaye da suka sace daga kauyuka.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa An kashe mutane 16 a Jihar Kaduna a wata sabuwar hari.

Sojojin sun bayyana da cewa sun kame mutane 24 da ke yadda sako da ‘yan ta’addan, masu basu wajen kwana dadai masu taimaka masu wajen sanar da su da harin da ke gaba. “An kuma karbi wayoyin sadarwan su da mika su ga jami’an tsaron ‘yan sanda don kara binciken su“

An gabatar a sanarwan da cewa an samu nasarar hakan ne a yayin da rundunar sojojin suka hari dajin Kagara, Gando, Fankama, Fete da kuma dajin Dumburum, inda aka haska wutar hari ga wajen buyar ‘yan ta’addan”

An ribato kayaki kamar bindigogin AK 47 kusan ashirin da bakwai, da wata bindiga da ake ce wa Magazines, kimanin, motar yaki da daman, baburar hawa, Mota, da kuma shanaye da aka sace.

“Ba a samu cin wannan nasarar ba, sai da hukumomin tsaron suka rasa Ofisa daya, Sojoji biyu da Danbanga daya daga dajin Kagara” inji rahoton.

Maj. Clement a cikin bayanin sa ya bayyana da cewa Kwamandan rundunar, Maj. Janar Olabanji Stevenson ya yi gaisuwar ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukan su a wajen harin, da cewa Allah ya jikan su, mutuwarsu kuma ba zai zama a banza ba” inji shi.