Connect with us

Uncategorized

2019: Kalli ranar da za a fara jarabawan JAMB ta bana

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A jiya Laraba, 13 ga watan Maris 2019, Hukumar JAMB ta gabatar da ranar da za a fara jarabawan shiga makarantan jami’a (JAMB) ta shekarar 2019.

Hukumar JAMB ta gabatar ne da hakan a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba daga hannun mai sanarwa ga hukumar, Mista Fabian Benjamin, da cewa za su fara jarabawar JAMB ranar 11 ga Watan Afrilu, shekara ta 2019.

Mista Benjamin ya gabatar da cewa jarabawar ta farko watau (MOCK) zai kasance ne a ranar 1 da watar Afrilu, 2019 a dukan kasa, kamin jarabawan ta biyu.

Naija News Hausa na da sanin cewa hukumar ta gabatar ne a baya da cewa zata fara jarabawar a ranar 23 ga watan Maris, 2019 kamin dada a yanzu suka daga shi zuwa gaba.

Ko da shike hukumar JAMB bata bayyana dalilin da ya sa suka daga jarabawar zuwa gaba ba, amma muna watakila a Naija News Hausa da cewa watakila hukumar ta yi hakan ne saboda zaben wasu jihohin kasar da aka daga zuwa ranar 23 ga watan Maris, saboda wasu matsaloli da aka samu a zaben da aka yi a baya, kamar yadda hukumar INEC ta gabatar.

Benjamin ya kuma shawarci wadanda suka rigaya da fitar da takardan MOCK din da cewa kada su damu da sake fitar da wani daga konfuta, da cewa suna iya zuwa da wanda daman suke da ita.

Ya kuma gabatar da cewa za a fara fitar da takardan gane rana, lokaci da kuma wajen ainihin jarabawan JAMB daga ranar 2 ga watan Afrilu, 2019.

“Duk wanda ya cika fom na JAMB ya tabbatar da cewa ya fitar da takardan cika fom din daga konfuta kamin ranar jarabawan. kuma kana iya yin hakan a ko ina a jihar da kake” inji Mista Benjamin a cikin sanarwan sa.

Ya kara gaba da cewa hukumar JAMB ta bada dama ga wadanda basu samu karshe cika fom din su ba da yin hakan har zuwa ranar Jumma’a, 15 ga watan Maris da missalin karfe goma sha biyu na dare (12PM) da za a rufe fegen cika fom din.

“Wannan daman an bayar da shi ne ga wadanda daman suka sayi fom din da basu samu karshe cika shi ba a baya” inji shi.

Karanta wannan kuma: An taras da gawa a wata rijiya da ke kewayan Makarantar Jami’ar UNIJOS