Connect with us

Uncategorized

Karanta bayani Gwamnan Legas game da Gidan saman da ya fadi kan yaran makaranta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Legas, Gwamna Akinwunmi Ambode, a yau Alhamis, yayi bayani game da gidan saman da ya rushe a birnin Legas.

Mun sanara a Naija News Hausa a baya da cewa wata gidan sama mai taki ukku a shiyar Ita-Faji ta Jihar Legas ta rushe akan ‘yan makaranta da malaman su hade da mazaunin gidan a ranar Laraba da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa Gwamnan ya ziyarci wajen da abin ya faru ne ‘yan awowi kadan da abin ya faru.  Ya kuma gabatar da cewa gwamnatin Jihar zata dauki nauyin wadanda suka rayu da ake wa kulawa a asibiti don samun cikakken lafiyar jiki.

An kuma bayyana da cewa mataimakin gwamnan, Dakta Oluranti Adebule, ta ziyarci asibitin da ake nuna kulawa ga wadanda abin ya faru da su, da kuma bada tabbacin cewa gwamnatin Jihar Legas zata tabbatar biyar dukan kudin kulawa ga mutanen da ganin cewa sun samu lafiyar jiki ta musanman.

Gwamnan ya bayyana da cewa an umurci masu gidajen shiyar tun a baya da cewa su rushe gine-ginen da ke a wajen tun lokacin baya, amma sun ki da hakan.

“Abin takaici ne da cewa ginin da ya rushe ba ainihin makaranta bane, gidan zama ne. kuma makarantar da ke kasar an kafa shi ne ba bisa kan doka ba” inji Gwamnan.

“Masu gidan yankin nan sun ki su bi umarni da muka basu na tare daga wajennan. Ba zamu janye ba daga kare rayukan mutanen Jihar nan, zamu tabbatar da cewa mun kula da rayuwar mutane da zaman lafiyar su a Jihar Legas” inji Ambode.

Karanta wannan kuma: Ga tsarin sunayan Gwamnoni, da Jam’iyyar da ta lashe zaben ranar Asabar